BARRISTER ASSAD
COMPLET EBOOK
KADAN DAGA CIKI
Alhaji Muhammad Ali babban Dr ne mutum ne d'an boko sosai asalinsa buzu ne amma 'a Nigeria ya tashi Allah ya basa ilimi sosai bayan kasancewar sa Dr kuma Professor ne yanzu haka yana da asibitin kansa, matar sa d'aya 'ya'yanta uku Ibrahim da Nabila sai kuma auta Sadiya amma suna kiranta Jalila kasancewar sunan mahaifiyarta ne da ita, Ibrahim da Sadiya sunyi karatu mai zurfin gaske gashi Allah ya basu baiwar k'wak'walwa kullum su suke d'aukan over roll students, Ibrahim yanzu haka ya kammala PHD d'insa yayi aure 'a chan Uk kasancewar 'a chan yayi karatunsa koda ya kammala karatunsa da first class upper ya fita shine best student of the year wannan dalilin ne yasa suka d'aukesa aiki!
Nabila kuma sai da ta kammala master's nata tayi aure lokacin tana 20years tayi aure ita ma Allah ya bata k'wak'walwa ita ma tana lecturing 'a ABU dan 'a Zaria tayi aure...ita ne the most youngest Lecturer 'a ABU English 'a bakinta kaman me dan Slang take yi......tun tana k'arama mahaifinta da mahaifiyarta basu yi wa 'ya'yansu Hausa sai dai English wannan dalilin ne yasa in suna speaking kaman 'ya'yan turawa, shima mijin nata mugun d'an boko ne shine Chancellor na school d'in
Jalila 'yar auta kam ba'a magana dan ita Allah bai had'a jininta da karatu ba kullum na 6 ko 7 take zuwa yayunta kam basu tab'a wuce first position ba, Jalila bata ji ko kad'an kullum sai an kawo k'ararta gida...Jalila sam bata ji gashi bata da mutunci ko kad'an ga rashin ji, ga rashin kunya, surutu, fitsara, fitina duk ita d'aya dan indai tana wuri sai ansan tana wuri, gashi tana da son hayaniya in tana abu wane 'yar daba!
Duk friend's nata maza ne shiyasa ita ma behaviour nata na maza ne
Duk zafin iyayenta sun rasa ya zasu yi da ita...dan mahaifinta yana da zafi sosai amma tunda Allah ya basa Jalila yayi sanyi gashi Allah ya d'ora masu sonta ta kad'an ba, amma basu nuna mata irin sosai d'innan saboda irin halin yaran zamani.....tana k'aunar iyayenta sosai ba kad'an ba wannan dalilin nema yasa take gudun b'acin ransu dan in ransu ya b'aci hankalinta mugun tashi yake yi koda ba ita ta b'ata masu rai ba in taga ransu ya b'aci sai ta zauna tayi ta yin kuka
yanzu she's 16years this year zata gama secondary school, amma sai ka ranste she's 14 dan wautanta is worst
Zaune take hannunta rik'e da littafi amma ba karatu take yi ba hankalinta na kan Tv sai taji motsi tayi pretending as if she's reading dan ace tana karatun exams,
Mami ne ta shigo palon tare da Daddy
"Baby girl karatu ake yi?"
Fake smile tayi tana jin dad'i tace
"Yes Dad"
Girgiza kai Mami tayi tace
"Am certain she's not reading, she's just ptetending"
Tuni ta fara hawaye
"Mami am reading fa"
Murmushi tayi tace
"Yawwa good girl reaction naki ya nuna kina karatu da gaske good girl"
Dafa kanta Daddy yayi yace
"I promise in kika yi k'ok'ari in your Exams i'll buy you latest iPhone da makeup kit"
Tsalle tayi ta fara yi masa godiya
Tun daga ranar Jalila ta zama serious kullum ka ganta karatu takeyi tsakaninta da Allah dama already wayanta ya lalace babu chating, kallo ma bari tayi...dan school d'insu ba'a bayar da Exco na Waec and Neco
'A haka har suka gama Exams Jalila ta dan nustu tana karatu koda Result ya fito Jalila tayi k'ok'ari sosai daga A sai B..A sunma fi yawa dan ita ma tana da k'ok'ari kawai karatun ne bata so...the next day Daddy ya cika mata alk'awari ya saya mata Makeup kit had'e da X d'inta ranar kasa bacci tayi dan farin ciki
Tun daga lokacin labari ya chanja Jalila ta chanja friends sai masu x ne friends nata, rashin ji ko k'aruwa yayi Daddy ya kai ta training na computer kafin 'a fara bayar da admission, Jalila kam da driver ya ijiye ta take k'arawa gaba yawo dan wannan new friends d'in nata fitinannu ne, gasu da shegen yawo kullum suna kan titi posting kam ba'a magana dan IG and Snap sun san da zaman Jalila, Modelling ma ta fara duk wasu photographers sun san da zaman ta...makeup artist duka dai hotunan ta sun gama zaga duniya
Rashin ji kam ya k'aru da kula samari dan duk wani matashin saurayi yasan da zamanta, samarinta basu irguwa....duk abinnan da take yi Daddy da Mami suna sane kawai sunyi mata shiru ne...may be they are up to something!
Zaune take 'a kitchen ta mik'e k'afa tana yanka Alayyahu duk ta b'ata wurin wane wata mara hankali Mami ne ta shigo tsoki tayi had'e da galla mata harara tace
"Wai Jalila yaushe zaki yi hankali? Yanzu yanka alayyahun shine kika b'ata duka kitchen d'in?"
K'asa tayi da kanta tana murmushi, tsoki tayi tace
"Aurar dake zanyi na huta na wannan iskancin naki"
Turo baki tayi tace
"Ni aure 'yar k'arama dani Allah ya kiyaye...Anty Nabila ai sai da tayi karatu aka mata aure"
Rankwashinta Mami tayi tace
"To fitsararriya ai sai ki zage ni"
"Kwarai da gaske aurar dake zamuyi ai kin sa ja'ira kawai" Taji muryar Baabaa mai aikin su tana shigowa
Murgud'a baki tayi tace
"Ai sai ki aurar d'in"
Rankwashinta Mami tayi tace
"Ohhh fitsararriya da Baabaa zaki yi?"
Murmushi Baabaa tayi dan sun saba yi da Jalila kullum sai sunyi fad'a kuma still suna shiri dan bakin Jalila bai yin shiru da sunyi fad'a zata cigaba da bama Baabaa labari in tayi banza da ita ko tana amsa mata Emm...sai ta bata hak'uri dan ta iya bayar da hak'uri ba kad'an ba...