JUYA complet - HAUSA EBOOKS -->

HAUSA EBOOKS

NQNia.blogspot.com Is a Premium Template Sharing Blog

JUYA

Littafin Feenat jafar
Complete

KADAN DAGA CIKI

.
1_A gaban mudubi take tana k’yali,ta shafa nan,ta shafa chan,ta mudubin kuma tana d’an k’allon ta cikin shi tana murmushi, ganin yadda mutuminta ya zuba mata ido ta ciki.
Juyowa tayi,yai d’ai-d’ai akan gado yana k’allonta, d’uk rashin k’yau na abu,toh mud’in kana muradin shi mai k’yau ne a wajen ka. Babban mamakin shi yadda ya kasa ganin munin Matarshi a kullum, yakan shafe “seconds” dan gano ta inda “Prettyn”shi ta gaza, kai ya girgiza, dan shi baiga makusa ajikinta ba ko kad’an.
D’uk a kullum dangin shi suna mishi gorin d’uk k’yawawan garin nan,amma ya rasa wacce zai jaju6o sai Fulera,ga ta “JUYA”,ta bare suce ko dan haihuwa taci darajar so,,d’uk ta tare gaba,ta tare baya, ta hanashi ganin d’uk wani makusa tata a gare shi,balle yai tunanin gazawarta na zama “JUYA”.
Asalima shi in d’ai zai tozali da Fureran shi”Pretty” toh yakan manta komai.
“Pillow” ya sake jawo wa,lokacin da ya g’yara k’wanciya yana cigaba da k’allonta, d’ai- d’ai da dak’ika d’aya baya fatan yaga “Pretty” ta barshi,yana matukar k’aunar ganinta kusa dashi. Bai aune ba ya ji ta hure mishi ido da bak’inta tana murmushin nan wanda ke sashi murmushi ko da bai shirya ba,, kamshin “lestrine” ya buge shi, had’i da kamshin alawarta ta kullum,”splash”. Take ya sau ajiyar zuciya, kan ya k’allota.
Hakika yana kara godiya ga Allah mad’aukakin sarki da ya bashi “Pretty” a matsayin “Matarshi” kuma “Sanyi ga Idanunshi”. Tabbas yana daga cikin maza masu t’sant’sar sa’a a rayuwa na samun “mace ta gari”,wacce ganinta kad’ai, ya isa wanke maka bak’in cikin rayuwa,har yai hamdala da mahaliccin shi,dan ya mishi baiwa,irin wacce ba Kowanne namiji ke da ita ba, a ganin shi,dan ya hanashi “D’a” bazai zamu ya masa butulci ba.
Murmushi ya sakar mata,kamar kullum ya fara yaba mata wankanta. “Kinyi k’yau sosai pretty, a kullum ranakun duniya kamar ana dad’a kawata min ke ne,kamar ki zauna nai ta k’allon ki kawai.
“Ko zaki fasa zuwa sunan?
Murmushin jin dad’i tai,gashi d’ai kullum irin kirarin nan tana shan su,amma baya hana taji dad’in jinsu.
Zama tai, tare da ruko hannunshi ta kai baki tai”kissing” take k’wa ya sauke ajiyar zuciya,tare da d’aura d’ayan hannunshi kan nata..
Tsaf ta riga da ta gama samo abinta cikin ruwan sanyi, ta riga da ta gama sanin d’uk wani “week points” nashi akanta, mai lafazi mai k’yau ce ita da sanyin murya, takan ko’k’arin tauna zance,sannan ta ya6a mishi”gold” da “lu’u-lu’u kan ta bashi.
Cikin salon ta da wata irin murya ta fara magana tana lumlumshe mishi ido da d’an lallashi. Ji yake mar rad’a take mishi a kullum.
“Kar kaji kom “Nawan” ni taka ce ai,k’walliyar ma taka ce, zan rintse ta ga ganin kowa,sai d’ai in mata y’an uwa na, badan sanin mahimmancin sunan nan a gare ni ba,da zan ta zama,kai ta k’allo na,har sai kace na ishe ka.. Ta karasa tana fari da idonta, take k’wa ya sau ajiyar zuciya.
Unguwa ko bai niyar barin prettyn shi ba,da kalam kawai zata sa ya firta “Toh”.
Kai ya girgiza kan ya tashi ya zira rigarshi.
Ita kuma ta sa hijab da Nikaf dan rufe k’walliyar.
Tafe suke a mota,suna ta faman firar duniya cikin nishadi,har ya faka a kofar gidan sunan,wanda matar K’aninshi take gare shi.
Hannunshi na cikin nata,tambayarta yake sai yaushe zai zo d’aukan ta? Ganan wasu na shiga,wasu kuma na fita a gidan sunan,sai d’ai in sun fito,maimakon su tafi,sai suja su tsaya k’allon su prettyn.
Tana shiga ta tsaya ta cire nikaf d’in, kan tai bangaren mai jego.
Da sallama ta shiga d’akin fuska sake, fal cike da jama’a, kowa ya zuba mata ido, ta samu gefen gad’on ta d’an dosa na,tana kula da hararar da wasu ke sakar mata,”ina yinin ku.. Fuska mai jegon ta yamitsa,kan tace”sai yanzu? Dad’i Miji.. Murmushi tai,dan tasan da ta tofa yanzu za’a fad’a mata magana. Cigaba tai, “shidai cin tuwon kishiya ramako ne,ehee. Kai ta k’ada, lalle mutum.
K’anwar mijin tace ta amshe,”ba Kowanne tuwan bane na ramako..kar ma kisa a ka,a yadda tai shirim d’in nan ne zaki sa rai? Baki ta ta6e,kan tace suna ga wata wai “JUYA” tashi tai “parlour” tana hararar prettyn,wacce ke mata murmushi...

DON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN SAI KU DOWNLOAD NASHI ANAN KASA

JUYA complet

Load Comments

Subscribe Our Newsletter

Notifications

Disqus Logo