BURIN HAFEEZ
littafin Aisha
KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN
Episode 1⃣
Tasss!! Kakeji ya wanketa da kyakyawan mari, cikin hargagi da tsananin masifa yanuna ta da d'an yatsa yace "ke dabbar inace? Kina gani lokacin da nake 'ko'karin kauce miki amma saboda tsabar dabbanci da 'kauyanci irin naki shine kike 'ko'karin shigemin, salon naje nabugeki kijawomin zuwa asibiti"
A gigice ta ri'ke 'kuncinta wanda yakemata tsananin rad'ad'i da azaban ciwo, batareda ta kallesa ba, cikin sassanyar muryanta tace "kayi ha'kuri, nima ba a son raina hakan yafaru ba, kaina ke tsananin min ciwo, hajijiya ce ke d'awaniya dani bansan lkcn da na tunkari motanka ba, kayi ha'kuri"
Tana fad'in haka tudu'ka tad'auki bokatin awaranta wanda yazube a 'kasa, ta ratsa ta gefensa tawuce, sakin baki yayi yana binta da kallo, cikin zafin rai yace "ke!!!! Zonan"
Batare da ta kalli inda yake ba tajuyo jiki asanyaye, qarasowa tayi gamida duqe kai cikin sassanyar muryanta tace gani, wani irin iska mai d'aci Hafeez yafurzar gamida xaro manya-manyan idanunsa fuska a hargitse yace ke waye ubanki agareni nan? Da har adalilina xaki xubar da kayan tallanki amma kikasa budan baki kice nabiyaki, damekike taqama stupid grl?
Wasu irin xafafan hawaye ne ke kwaranya akan kod'ad'iyar fuskarta, cikin nuna rashin jindadin kalamansa tace" kai kuwa bawan Allah kai wanne irin mutun ne? Naga tunfarko nabaka hakuri sannan kayan sana'ata da suka xube bana buk'atar kabiyani" meka dauki kanka?
Toh bari kaji niba irin yan'matan nan bane masu son cece kuce akan titi ba, sannan kana mgnr cewa waye ubana' umhm ubana shi ba kowa bane, kmr yadda kasani baxai iyaja da mnya kmr Ku ba. Tana fadin haka ta gyara jemammen silifas dinta wnda yake qoqarin fita a qafarta tacusa qafarta ciki tafara tafiya cike da sanyin jiki' cikin xuciyarta kuwa wani irin baqinciki da qunci gamida d'umbin damuwa ke d'awainiya da ita.
Abangaran Hafeex kuwa ko k'wak'waran motsi yakasayi sbd tsananin mamaki da ya kamashi kasancewar tunda yake ganin yan mata kala-kala masu aji da marasa ajin babu wacce ya tab'a ciwa mutunci ta maida mishi da marta sai wannan jamammiyar talakar yarinyar" cikin tsananin fushi Hafeez ya fara takawa da nufin isa gurin wannan yarinyar, ae kuwa da sauri wata kyakyawar matashiyar yarinya tafito acikin motar da sauri gamida riqo hannunsa tace "plss Yaya Hafeex don't do dat 4god sake, tundaxu ina kallonku fa kasanar da ita laifinta Kuma wannan baiwar Allahn ta amsa laifinta har tabaka hkri" plss yaya kaxo mutafi gda ni ynwa nakeji gabadaya am vry tied,
Fuskan nan ta Hafeez kuwa kokad'an babu fara'a yace look Balkisu pls ki k'yaleni inje inkoyama yarinyan nan tarbiyya,sbd na lura kokad'an bata da manners, cike da shagwab'a Balkisu tafara bubbuga qafafunta kmr xatayi kuka "plsss yaya nidai ka kyaleta kaxo mutafi gda," Hafeez yasake waiwayan wannan yarinya amma tuni tab'acewa ganinsa..wata uwar kwafa yayi gamida Jan tsaki ba haka yaso ba dan haka bashida wani xab'i dayawuce yashiga mota sutafi.cikin qasan xuciyarsa kuwa wani irin haushine yacikasa sbd gabadaya haushin knsa ma yakeji da bai qara marinta ba.
Al'asfar Restaurant yawuce da ita kai tsaye, sbd Hafeez Sam bai qaunar ganin Balkisu na complain akan yunwa, abinci kala-kala masu kyau da tsada yasa aka kawo mata. Taci sosai"shikuwa Hafeez sbd b'acin rai koh abinci yakasaci, babu yadda Balkisu batayi akan Yayan nata yaci abinci ba amma Sam yaqi., hakanan Balkisu tadaure itama tadanci abincin ba wai don ranta yaso ba..
Jiki a sa6ule suka nufi gda, shigarsu keda wuya Hafeez yanufi sashensa cike da 6acin rai' abangaran balkisu kuwa nadama ne gamida Danasani fal acikin xuciyarta.domin kuwa ita kanta tasancewa itace silar wannan fushin nasa
Sbd tahanashi aikata abinda take ganin shine dai-dai,
Acikin wannan dare kuwa daga balkisu har Hafeez babu Wanda yaruntsa, sbd kowa da tunanin da yakeyi cikin zuciyarsa. Abangaran Balkisu kuwa talashi takobi gamida alqawarin sai tanemo wannan yarinyar a dukk indatake, sbd tabama yayanta damar cikar Burinsa.
Da wannan tunanin nannauyan bacci yyi awon gaba da Balkisu........
DOMIN KARANTA CIKAKKEN LITTAFIN SAI KI DOWNLOAD NASHI A NAN KASA