RIBAR BIYAYYA by Sawwama page 1,2,3 - HAUSA EBOOKS -->

HAUSA EBOOKS

NQNia.blogspot.com Is a Premium Template Sharing Blog

💖RIBAR BiYAYYA💖

This Novel is downloaded from www.dlhausanovels.com.ng for more hausa novels including love and adventure hero, legend and mystry,tale hausa novels just visits our site www.dlhausanovels.com.ng to download for free

By Sawwama A. 

Page 1.

 _Bismillahir rahmanir rahim_

Kanta a duk'e yake tana k'ok'arin karatu amma hakan ya faskara,duk yanda tayi k'ok'arin cire hankalinta da tunaninta akan abinda ke faruwa a tsakar gidansu tsakanin mahaifinsu da yayarta abin ya faskara.

Tsaki taja tare da toshe kunnuwanta da yatsunta dan jin irin dukan da baba ke yiwa yayarta khadeeja yana fad'in " wallahi ban haifi abinda zai fi k'arfi ba dan rashin mutunci ni zaki kalla kice ba kya son d'an 'yar uwata?"

Ita kam bakinta bai mutu ba ihu take tana " fad'in ni dai bana sonshi kuma wallahi ba zan aure shi ba" shi kuma baba bai fasa dukanta ba.

Kusan kullum abinda ke faruwa a gidanmu kenan kullum sai ya daketa yace sai ta auri d'an 'yar uwarshi ita kuma ta dage bazata aureshi ba. Ni kaina mamakin yanda adda adija ta fitsare nake dan baban mu wani irin mafad'acin mutum ne hakan yasa duk muke tsoronsa kai ba mu da muke yaransa ba har yaran anguwa na tsoronshi dan shi in yaga yaro na abu mara kamashi yake ya tsutsula mishi dorinarsa da take rataye d'akinsa hakan yasa ake tsoron sa sosai amma abin mamaki adda adeeja tsoron nan ya kau bata damu da irin dukan da yake mata ba wanda tun yana dukanta da dorina har ya koma da icce amma ita ta tubure tana kan bakanta na baza ta aureshi ba ya mata yaro ita tana da wanda take so,ya hana ta fita ya hanata zuwa makaranta amma hakan bai ko sa ta sakko ba. Duk abinda akeyi mamanmu bata tab'a kula su ba harkar gabanta kawai take yi in tana zirga-zirganta yake jibgar adeejan bata ko d'aga kai ta kallesu tana gamawa kuma zata k'ulle d'akinta.

Ajiyan zuciya ta sauke ta mi'ke ta je k'ofar d'akin tare da d'aga labulen abin takaici baba ta gani yana sunkuye yana d'aure 'yar uwarta kan adeejan a duk'e tana kuka ciki ciki saboda yanda muryanta ya shak'e gefe guda kuka mama ce ke tsugune tana alawlan magriba, hawayena ya gangaro kan dakalin fuskarta na tausayawa 'yar uwarta baba na fita sallah tayi saurin zuwa gaban adeeja ta tsuguna tare da d'ago hab'arta idanunta duk sun kumbura sun koma ciki saboda azabar kukannda take yi kullum.

Murmushi ta sakar mata wanda hakan yasa hawayen fuskanta ya k'aru cikin kuka tace " adda adeeja ki taimaki rayuwarki ki karb'i zab'in baba wata rana zaki ci *ribar biyayyan* da kika mishi." Wani murmushi ta kuma yiwa kanwarta murya a shak'e tace " Fateema ke yarinya ce baza ki gane halin da nake ciki bana son shi ni Abdulhameed nake so shine burin zuciyata shi nake fatan inyi rayuwar aure da shi ba wannan d'an yaron ba"

Kafin tayi wani magana mamansu ta k'wala mata kira hakan yasa ta mik'e da hanzari ta tafi d'akin maman sallah tayi mata umarnin taje tayi.

Washegari fateema na shirin makaranta hankalinta na kan adeeja dake kwance tana baccin wahala ta duk'unk'une a cikin bargo da alama sanyi da zazzab'i sun shigeta dan jiya abin na baba ya wuce tunaninsu dan a tsakar gida ya barta ta kwana duk irin sanyin da ake tsulawa a garin jos na farkon watan sha biyu. Wuyanta ta tab'a taji shi zafi zau gashi sai rawan sanyi take d'an tsaki taja ta fito d'akin mamansu ta gaya mata toh shine abinda maman tace.

Haka ta dawo ranta na k'una yanda maman bata nuna b'acin ranta kan abinda baba ke yiwa adeejan ai ba shi kad'ai ya haifeta ba ana auran nan dole ne? Haka ta cigaba da shirin makarantanta cikin blue din skirt dai dai guiwa da farar riga sai blue din waist couth sai farar doguwar safa da ta saka har guiwa sannan tasa wan guntun safan kafin ta saka sandal dinta na fata ta saka farar hijabi gayu ta fito d'as da ita.

Ko kafin ta fito daga d'akin har ta jiyo muryar 'yar uwarta kuma abokiyar tafiyanta charity tana gaishe da mama cikin yaren su na birom, fitowa tayi suka kama hanyan makarantar au Bishop collage a k'afa suke tafiya kasancewar baau da nisa sosai da makarantar.

A hanya charity ne tace "wai har yanzu baban ku bai hak'ura ya bar adeeja ba ?" Bata bari ta ansa ta ba tace "kai ku kam hausawa kuna da matsala wallahi wai ace mutum da rayuwarsa amma ace za ayi mishi dole, adeeja d'in ma yaushe ta kai aure just 17 years in ss2 ace za ayi mata aure for Christ sake this is not fair. Ita dai bata kula ta ba hankalinta na kan yanda zata taimakawa 'yar uwarta.

Charity dince ta kuma cewa "ni gaskiya na gaji da gani sist adeeja haka zan sami ngo d'inmu in gaya mata abinda ke faruwa in yaso sai ta sami ngo d'in ku ta gaya mata tayiwa baba magana what he is doing to adeeja us not fair just because he gave birth birth to her does not mean he have control over her(abinda yake yiwa adeeja ba adalci bane dan ya haifeta ba yana nufin yana da iko da rayuwarta bane)"

Duk da kalamanta sunyiwa fateema zafi amma hankalinta yafi raja'a akan cewan da tayi zata gayawa kakarta ta samu kakarsu da magana dan dama duk abinda akeyi kakarsu mahaifiyar mamansu bata sani ba maman ta hana a sanar mata tace 'yarsa in yaga dama ya kasheta, yanzu kuma in charity ta fad'a mata ai shikenan sai tazo ta tsawatarwa da baba.

Da wannan shawaran suka isa makarantarsu suna shiga gate d'in da david ta fara cin karo da alama sune da duty duk seniors d'in suka fara kiranta da sunan tsokananta dan ita mai farin jini ce a wajeb d'alibae makarantar da malamai Chinese girl chinese girl  turo dan k'aramin bakinta tayi tana cire hijab d'in wuyanta ta tura a cikin jaka. David ne yazo gabanta yana magana k'asa k'asa yace "how far?" "Fine " shine abinda tace tayi gaba dan ta tsani yaron arnen da ya sata a gaba da sunan so toh ita d'inma guda nawa take mtswww ta ja tsaki.

Yammacin ranan tana zaune tana assignment d'inta adeeja na kwance dan har lokacin zazab'in bai saketa ba taji sallamar kakarsu da sauri ta rufe littafin ta fita a guje ta d'ane 'yar tsohuwar tana murna.

B'anb'areta tayi daga jikinta tana fad'in "oh ni sakeni kaman baki san hanyan gidana ba sai mutum yazo ku fara murnan k'arya" dariya tayi ta k'ara mannewa jikin kakar tasu tace " haba ngo na kin san school ba barin mu yake ba in na dawo ga assignment wanki uniform karatun islam weekend kuma asabar da lahadi kinga ai ba lokaci"

"Toh naji kanari ai ke daman ba a k'ureki ko da yaushe kina da excuse" dariya tayi suna shiga d'akin mama

Ko da mama ta fito daga ban d'aki bayan sun gaisa da ngo masifa ta rufeta da ita cikin yarensu na birom ta inda take shiga ba tanan take fita ba tun ba da taje ta ga yanda jikin khadeejan ya kumbura ba ga zazzafan zazzab'i da take fama da shi ba wanda ya kulata.

D'aukanta tayi ta kaita asibiti tare da rakiyar fateema aka mata allura aka bata magunguna sannan suka dawo gida inda suka tarar da baba ya dawo daga aikinshi na drivern taxi.

K'ulewa d'aki suka yi da ngo tayi ta mishi nasiha tare da fad'a a haka ta samu ta shawo kanshi ya hak'ura zai barta ta auri wanda take so da sharad'in ba ruwanshi duk abinda yaje ya dawo tunda ita taurin kaine da ita tak'i d'an uwanta ta dage sai bare mai mata, haka dai tayi ta lallab'anshi kasancewan yana girmama surukar nashi ya haqura.

Zaune yake bayan tafiyan ngo yana tunanin ta yaya zai fara runkarar yayarshi da batun y'arsa bata son d'anta da ya nuna yana sonta shi kam ya shiga uku ya haifi abinda ya tozartashi me k'watanshi a hannun hajiya sai Allah dan duk masifarshi ta fishi tunda abin a jininsu yake.

'Yar wayarsa ya zaro touchlight phone ya danna numbern baba k'arami bayan sun gaisa yace mishi in ya sami lokaci yazo yana nemanshi amsa mishi yayi da toh inshaa Allahu zai zo.

Tsaki yayi tare da jefar da wayan bayan ya gama ansa kiran kawunshi shi wallahi yayi dana sanin cewa yana son yarinyan nan shi fa dama ba wai ya wani zurfafa akan sonta bane kawai tana burge shi ne gata da kyau jan ajinta ya k'ara janyo hankalinshi kanta baiyi zaton zata k'ishi ba da bai furtawa hajiya yana sonta ba gashi yanzu ta k'wallafa rai da wannan had'in wani tsakin ya kuma ja ya rungumo pillow dinshi yan so yayi bacci amma ranshi sai suya yake baya son abinda zai tab'a ran hajiya wallahi da yace a bar maganan auren nan toh yanzu sai hajiya ta k'ullace ta yanzun ma ya aka k'are cewa take uwarsu ce ta zugata tak'ishi bayan shi bai ga alamun k'inshi a wajen mamansu ba amma zai samu lokaci yaje jos d'in yaji koma meye. 

SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖

By Sawwama A. 

Page 2.

Kallon mamaki kawai fateema ke bin adeeja dashi ganin yanda ta sake tana ta hirar soyayya da saurayinta Abdulhameed sai shagwab'a take zuba mishi kaman ba ita take shan jibga ba a ranta tana tausaya mata rashin miji kaman baba k'arami au yah sagir ta manta ya rok'eta kar ta dinga kiranshi baba k'arami kaman yanda sauran zuriyarasu keyi ko in ce mafi yawancin su.

Tuno da randa ya fara zuwa garin tayi wata biyu da suka wuce kenan.
Wani yammaci ne suka ji dirin motoci biyu a k'ofar gidansu daganan kuma suka ji muryar baba na shigowa da wani fuskan mama ne ya fad'ad'a da fara'a ganin wanda suka shigo da baba.

Kama hab'a tayi tace" ikon Allah baba k'arami kaine ka girma haka" murmushi yayi ya tsuguna yana gaisheta su kam yaran sai kallonsa suke da mamaki dan basu wani sanshi ba gwara ma adeeja tana ji kaman ta sanshi suma gaisheshi suka yi.

Nan da nan mama ta fara hidima da shi abin ya k'ara basu mamaki yanda mama bata bar musu hidiman ba dakin baba duk suka shiga saboda yayyafi da aka fara kuma suna son jin k'wak'waf d'in waye wannan d'in.

Fateema kam da ta kasa hak'uri dan taga sai hiransu take da alama dai daga bauchi yake dan taji baba na tambayanahi su hajiya masifaffiya sunan da suka saka mata kenan

"Baba wai ahi wannan d'in waye?" Fateema ta tambayi babansu  dariya duk suka yi mama tace" toh kaji kai baba k'arami saboda rashin zumunci k'annenka basu sanka ba."

Murmushi yayi yana shafa gashin kanshi bak'i sid'ik da yasha gyara da ka ganshi kaga gashin fulani yace " mama ai suma basu da zumuncin dan ban tab'a ganin sunje bauchi hutu ba"

Tab wa zaije gidan hajiya masi..." Pap mama ta buge bakin fatima jin tab'okaran da take shirin yi musu sarai ya gane me yarinyan take shirin fad'a a zuciyarsa yace ator ba dai tace juninta mita ba yaushe yara zasu so zuwa gidan tana cewa an raba ta da 'ya'yan d'an uwanta a fili kuma yace " ai kuwa fateema yanzu kin kula da bauci kenan."

"Hmmm" shine abinda tace dan tana tsoron yin wani magana mama ta k'ara buge mata baki amma da ta tofa.

Kwanan sagir biyu a jos a kwanaki biyun nan sun saba da fateema sosai dan shegen surutu gareta da abin dariya shi d'in kuma an dace mutum ne mai sauk'in kai gashi da barkwanci sai su zauna suta shiririta adeeja ce dai bata shiga shirginshi dan acewarta ya fiye rawar kai da shegen kallo ita bata son raini.

Suma basa kulata su sha kallonsu a laptop dinshi su ji wak'a ranan yake ce mata yaji wani wak'a mai dad'i da aka yi da sunanta tsalle ta daka ta tsuguna a gabanshi tace "wakar sabo ne ? Dan akwai wani waka da na sani da ina son wak'an sosai". Yace "gaskiya ban sani ba nima ji nayi a wayan wata k'awata" kallonshi tayi tana d'an hararanshi ta gefe tare da murmushi a fuskanta ta nunashi da d'an yatsanta tace a wayar budurwarka ko" dariya yayi sosai yace " wa yace miki a wayan budurwata naji k'awata nace me idon y'an china kawai" turo baki tayi ta sa kukan shagwaba tace wai ni me yasa ake had'a ni da 'yan china ne ?" Dariya ya kuma yai yace saboda idonku iri d'aya kuna kama amma dai kinfi kama da yan korea da d'an k'aramin pink bakinki." Kukan shagwaba ta sa tana bubbuga k'afa can kuma ta tuno tace to ka sa min wak'an ni dai wayarsa ya ciro yace" bari ince ta turo min a whatsapp dan ban da ita ni a wayana" bayan ya kira yace ta turo mishi ne yace" toh yi min wancan kafin.ya shigo inji ko shine."

Zama tayi a gabanshi ta tank'washe k'afa ta fara rero mishi _" fatima bintu fatima sai wata rana so mafarkine da ba tabbas ba bankwana bintu sai wata rana kukan zuciya da bana ido ba_ " tafa mata ya fara ai yace "iyyeee lallai kam bintu wak'an da dad'i amma ban tab'a ji ba yawwa wannan d'in ma ya gama downloading" danna mata yayi muryar m sharif ya fara amon wak'an _zahra zahra zahra_ ihu ta sa bayan ta gama ji tace "wallahi wannan yafi dad'i haka dai suka ta shirmensu wani sa'in da baki zai dinga mata wak'an _zahra zahra zahra kece sarauniya zahra_ ita tayi ta juyi tana kad'a mishi k'aramin waist d'inta.

B'angaren karatu ma da ya tab'ata yayi mamakin kwanyar yarinyan shi yasa suka k'ara shk'uwa. 

Ko da wasa adeeja bata shiga shirginsu har ya gama kwanakinsu ya tafi.

Sai me sai ga hajiya masifaffiya ta zo da kanta acewarta autanta yaga mata a gidan wai khadeeja yake so kowa yayi farin ciki ba ma kaman fatima.

Bayan tafiyan hajiya ne adeeja ta tayar da borin bata sonshi ya mata yaro gashi d'an kauye da shi baba yayi masifar yayi fad'an yayi nasihar taki shi ko da bai d'aukan wargi tuni ya fara had'a mata da duka haka bai sa ta canza ba.

B'angaren fatima tayi ta kod'a mata halayenshi rufeta tayi da masifa tace "ke kije ki aureshi mana ni nace bana sonshi ko ana dole ne?"

"Adda adeeja to me yasa ba kya sonshi gashi d'an gayu kyakyawa zaki ce mishi d'an kauye da idanunshi masu kyau manya"

"Dallah can rufa min baki mayyar manyan ido dan ke kam da zakiyi maita da masu manyan ido sun shiga uku shegiya kinayi da wasu k'ananan idanunki a wajen Allah ma shi yasan me ya gani ya hanaki manya ido ya baki na 'yan chinese" ranta ne ya b'aci taji haushi zagin da adeejan tayi mata toh ai dai *bani nayi kaina ba* da zaki dinga zagina dan na gaya miki gaskiya" ta murgud'a mata baki da gudu ta fita ganin ta hayayyak'ota tana shirin kai hannu jikinta.

Ajiyan zuciya ta sauke a fili tace" Allah sarki bah k'arami au ya sagir Allah ya kawo maka mai sonka abokina" wata uwar harara adeeja ta wurga mata tare da jefo mata kofin dake hanunta " Allah ya isa tace da karfi ta fita tana kuka dan taji zafin kofin silvern da ta wurga mata a goshi da baba suka ci karo yace" ke kuma fa?" Shaf ta manta daman yana cike da adeejan ta gaya mishi abinda adeejan tayi mata.

A fusace ya shiga d'akin ya zabzabga mata mari yana fad'in dan ubanki karya tayi yarinya sai taurin kai me kunnan k'ashi  kuma ki gayawa shi saurayin naki ya turo magabatansa kije can ku k'arata tunda shi kika zab'a ki bar min gida." Ya fita yana me cigaba da bambami take tayi dana sanin fad'a mishi dan tana son y'ar uwarta d'akin ta koma ta durk'usa gabanta tace" adda am kiyi hak'uri ban san zai dakeki bane" murmushi tayi tace ba komai k'anwata zan fad'awa hameed ya turo inyi in bar muku gidanku, rungumeta tayi tana  kuka. 

Tuk'i yake yana cikin tsananin farin ciki zai je yaga k'awarshi mutuniyarshi suje su d'an tab'a dramar su wani b'angare kuma na zuciyarsa na cike da fargaban dalilin kiran kawun nashi k'ile y'ar taurin kan ta amince ne shi fa ba zai yarda ayi mata dole ba dan baiga ribar auran wanda bai sonka ba kazo kana wahala dashi,dariya yayi tuno irin taurin kan yarinyan ta nunawa kawu shi ya haifeta itama bafulatana ce. A bakin anguwan ya ajiye motar gurin masu wankin mota ganin irin k'urar da tayi kaman ba a wanke motar ba kafin ya fito da ita amma k'urar hunturu ta bud'eta. Da k'afa ya k'arasa gidan ya kwad'a sallama.
💖RIBAR BIYAYYA💖

By Sawwama A. 

Page 3.

Fatima na zaune a kan dakalin cikin gidan tana wankin kayanta mama kuma na tsinke ganye adija na d'aki dan tunda abin ya faru zaman tsakar gidan ya gagareta.

Sallama yayi cikin muryarsa mai cike da aminci tsalle fatima ta daka sai gata a gabanshi tayi kaman ta rungumeshi sai kuma ta fasa ta tsaya tana yarfa hannu tana ta washe baki dogon hancin ta ya ja yana dariya yace me idon china.

Bakinta ta turo ta juya zata tafi hannunta ya riko yana gaishe da mama ta amsa amma ta kasa had'a ido da shi tana jin kunyan abinda yarta ta mishi,baba ne ya shigo da sallamarsa aka gaisa sannan suka shige d'aki mama tasa fatima d'aukan abinci in kai musu. Bayan sunci abinci sun gama Nasiha baba ya dad'e yana mishi kafin ya bashi hak'uri da cewa yarinya tak'i Allah ya kawo mishi wata cike da ladabi yace ameen baba wallahi ba komi ai matar mutum kabarinsa wani bai auran matar wani. "Haka ne haka ne baba k'arami Allah yayi maka albarka" ya amsa da "ameen baba ni zan wuce dan ban zo da niyyan kwana ba" toh shikenan babana Allah ya tsare hanya. Yace "ameen yana mik'ewa sallama ya masu hannu ya mik'o mata yace fati zoki rakani zan tafi mak'e kafad'a tayi tace uhm uhm ba inda zan rakaka tunda bazaka kwana ba" murmushi yayi ya juya yace toh shikenan ni na tafi tunda bazaki rakani ba ya juya ya tafi kallonshi take kaman wacce aka hanata binshi har ya fita a gidan. Bayan fitanshi baba yayi wani tunani lek'owa yayi daga d'akinshi yace fatima maza kira min yayanku kafin yayi nisa da sauri ta tashi har d'ankwalinta na fad'uwa amma bata tsaya d'auka ba, fita a gidan tayi da gudu can ta hange shi yana tafiya da gudu ta bishi tana kiran uhmmmm bah k'arami uhmmm kai kai uhmmmm yah sagir juyowa yayi da sauri ta k'arasa gabanshi tana haki. Kallon k'aramin figure d'inta dake gabanshi sai kanta ba d'ankwali sai dogon shukunta  da yake nuna alamun warewa ko kuma rashin kamuwa jujjuyawa yayi yaga ba wanda hankalinshi ke kansu kasancewar  anguwar ba musulmai sosai yace" k'awas ya dai kin biyoni rakiyar ne ko d'ankwali babu?"

Shafa kanta tayi tace " wallahi fad'uwa yayi ni kuma ina sauri kar ka b'ace min baba yace in kiraka inace ma a mota kazo kar kayi nisa" kai ya kad'a yace ai na bar motar a bakin hanya ana wanke min" haka suka k"arasa suna hirarsu. Baba ne ya kalleshi bayan ya shiga d'akin ya zauna yace" babana dama wata shawaran na yanke me zai hana ka komo kan fatima tunda ita bata da wani damuwa asalima bata san meye soyayya ba. Gabanshi ne ya fad'i jin batun kawun nashi a kasalance yace " kawu baka ganin za a shiga hakkin yarinyan da da karatunta? Baka ganin tayi k'ank'anta da aure?" Murmushinsu na manya yayi yace " ko d'aya fatima dai rashin jikin girma gareta amma ai ta isa aure shekara goma sha biyar aiko ta kai aure watan d'aya zata cika shekaru goma sha biyar mamakine ya k'ara cika sagir jin wai y'ar shekara sha biyar ce ta kai aure ai ko a karkara sai haka shifa ko da yace yana son khadeeja ba wai yana nufin suyi aure nan take bane shima d'in ai yaro ne gaba d'aya shekarunsa 26 kuma so yake yaje ya karo karatunsa zuwa phd.

"Kayi shiru babana ko baka son fatiman ne daman nayi k'wad'ayin had'in zumuncin ne kar kaji komi in baka sonta ka gaya min" ah ah baba Allah yayi zab'in alheri zan sami hajiya da maganan kafin kazo.

Haka ya musu sallama fateeman ta fito raka shi taga duk jikinshi a sanyaye hannunshi ta kamo kallon cute face d'inta yayi yace " ya dai mai suffan y'an korea?" Zaro idanu tayi tace" au na tashi daga mai kama da 'yan china na dawo 'yar korea?" Murmushi yayi kawai duk da k'arancin shekarunta ta san da ciwo ace ba a sonka marairaice fuska tayi ta kirashi da sunan da ta san yafi son a kirashi da shi wato sunansa na gaskiya "yah sagir kayi hak'uri k'ilan ba alkhairi tsakaninku ne shi yasa abin bai working ba kayi hakuri Allah zai kawo maka  wacce ta fita hali da komai wacce zata kawo farin ciki rayuwarka, ka daina damuwa kaji ta k'arasa maganan kaman zata yi kuka.

'Dan dogon hancinta yaja yace wa yace miki na damu ni ai har na sami matata" alhamdulillah" shine abinda tace. Sai yaso yaji cikinta dan yaran yanzu baka shaidansu mussaman akan soyayya " ke kuma waye saurayinki" ya tambayeta a dai dai lokacin da suka iso wajen motarsa dafe k'irji tayi tace "ni shegiya inji d'an daudu ina ni ina wani saurayi" dariya yayi sosai ya d'an jujjuya ya duba yanayin anguwan yace ke dai gaki baki girma cikin hausawa ba amma ya aka yi kika iya hausa haka" itama dariya tayi ta rufe idonta tace "ai ina zuwa islamiya a kwana shagari kuma ai kaga anguwan hausawa ne kuma akwai wata yarinyan ajinmu in malam bai shigo ba tayi ta karanta mana littafin hausa. Had'e rai yayi yace ashe ma ba karatu kike zuwa jin karatun littafin soyayya ke kai ki da sauri t girgiza kai tace ah ah ah ba littafin soyayya bane irin su iliya d'an mai k'arfi da magana jari ne fa kuma ma sai in ba malam a ajin" "duk da haka ai gwara kuyi muraja'a" 

Haka suka yi sallama ya kama hanya yana me dana sanin fara furta kalman so akan khadeeja da yanzu bai shiga tsaka mai wuyan nan ba
💖RIBAR BIYAYYA💖

By Sawwama A. 

RIBAR BIYAYYA by Sawwama page 1,2,3

Load Comments

Subscribe Our Newsletter

Notifications

Disqus Logo