[kiwon lafiya] Waiwaye a tarihin Coronavirus - HAUSA EBOOKS -->

HAUSA EBOOKS

NQNia.blogspot.com Is a Premium Template Sharing Blog

WAIWAYE A TARIHIN CORONAVIRUS

*****

Yanzu dai sunan Kwarona Bairos bai zama bako ba kasancewar ana ta yayata al'amarinta a kafafen yada labarai. Wasu na ganin cewar a wannan karon ne kadai aka samu irin wannan cutar, sai dai a binciken da na yi an jima da sanin ta a duniya.

Ita wannan cutar tun jimawa an san da ita kan cewar tana shake numfashi da haddasa zazzafan zazzabi da mura da tari da kuma lalata huhu da hanjin mutum ko dabba. Duk lokacin da aka samu bullar cutar sai a yi mata wani lakabi daban, ta kwanan nan dai ana kiranta Covid-19.

A 2005 wasu kwararun likitoci suka yi bincike a karkashin Dakta Kahn Jeffery. Sun bayyanan a wata mujallar likitoci mai suna, 'The Pediatric Infectious Disease Journal' cewar, an fara gano cutar Coronavirus a cikin shekarar 1965. Ita wannan an yi mata lakabi da B814. Daga nan aka yi ta samun bullar cutar daga lokaci zuwa lokaci.

Likitocin suka ce daga shekarar 2003 zuwa 2005 an samu bullar cutar har sau biyar. Coronavirus ta farko an rada mata sunan SARS wadda ta bulla a China cikin 2003 kuma ta halaka mutane 22 - 24. Ta biyu an yi mata lakabi fa NL63 a cikin shekarar 2004 inda ta bulla a Netherlands kuma ta kashe mutane 32. Ta uku ma a kasar Netherlands din ta bayyana inda ta kashe mutane 33 duk a 2004. Ta hudu kuma a yankin New Haven ta bayyana cikin 2005 inda ta kashe mutane 34. Ana mata lakabi da HCoV-NH. Sai ta biyar da ta bayyana a Hong Kong ta halaka mutane 35. Ita ana mata lakabi da HKU-1.

Haka kuma a tsakanin 2008 zuwa 2019 an samu bullar wasu irin Coronaviruses da ake wa lakabi iri - iri kamar, OC43, 229R, COVid - 12 da sauransu. Babbar coronovirus daga cikinsu ana kiran ta MERS-CoV watau 'Middle East respiratory syndrome - Coronavirus'.

Likitan kasar Masar, Dakta Ali Mohamed Zaki ya bayyana cewar ana iya samun cutar a jikin rakuma da aladu da kuma Jemagu. Ya kuma kara da cewar kwayar halittar wannan cuta yana da girma fiye da sauran kwayoyin cuta.

Sai dai da alama Covid-19 ta fi tsanani kuma ta fi girgiza al'ummar duniya ganin yadda take yaduwa da sauri kuma take halaka mutane cikin hanzari. Da alama kuma a wannan karon cutar ta bayyana da karfinta fiye da baya. Kuma da alama kamar ba a yi tanadin taron ta ba.

Wasu al'umma suna ganin da gangan aka kirkiri wannan cutar tun zamanin yakin duniya na biyu, sannan aka cigaba da wanzar da ita a lokacin yakin cacar baki. Shugabannin duniya suna sane da makami mai guba da Amerika da Rasha suka mallaka, ba abin mamaki ba ne a ce tun asali an kirkiro cutar ne a dakin gwaje-gwaje. Haka kuma ba zai zama abin mamaki ba idan mutane da dama sun san da sunanta a baya kafin yanzu da sunan ya zama ruwan dare.

Kuma ba zai zama abin mamaki ba idan an samu wasu marubuta a baya sun yi hasashen afkuwar cutar a shekaru masu yawa. Wannan baiwa ce ta marubuci kamar dai littatafai irin su 1984, Godfather, Class 1999 da sauransu.

Mu dai anan ba abin da za mu ce sai mu roki Allah ya kare mu da irin kariyarsa. Ya inganta lafiyarmu ya duba raunin shugabanninmu yadda cutar za ta wuce mu ba tare da kawo mana wafta ba.

-Danladi Haruna
19th March, 2020

[kiwon lafiya] Waiwaye a tarihin Coronavirus

Load Comments

Subscribe Our Newsletter

Notifications

Disqus Logo