Fanke
Abubuwan hadawa
- Fulawa
- Sugar
- Yeast
- Mai
Yanda ake hadawa
Da farko uwargida za ki tankade fulawarki a roba mai kyau mai murfi.
Sai ki zuba yeast da sugar da ruwa ki kwaba ya kwabu sosai(ya yi ruwa-ruwa in da zai rika kamun hanu) sai ki rufe a wuri mai dumi.
Ya sami kamar awa 1 ko 2 , idan ya yi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mai ya yi zafi.
Anan sai ki rinka deban kullin da ludayi kina sawa a cikin mai kina soyawa ya yi jan suya. Ana iya ci da shayi ko wani lemo
Sai mun hadu a girki na gaba.
Na gode