littafin gwarzon marubuci Bala Anas Babin Lata
An buga littafin a shekarar 1991
Farashi 200 naira
Published at okadabooks
About book
Sankon mai gidana Abba shi ne ya soma gaishe ni a daidai lokacin da na shigo garejin akan Kawasakina maras salansa. Na je na kafe babur din a karshen gini daura da ofishin Abba. Sannan na nufi wajen da yake yana ta fama da wata tsohuwar lada. Kwanansa biyu yana aiki akanta. Amma har yau bai yi dace ya kammala gyaranta ba.
Mai gida Abba gajere ne mai kaurin jiki yana da sanko, ban taba ganin mai dogon sanko kamar nasa ba, tun daga goshi har keya, in rana ta haska shi daukar ido yake yi kamar madubi. Amma bai damu yasa masa hula ba.
Yana saye da shudiyar rigar kaki watau rigar aiki, ta yi bakikkirin da maikon mota.
“Barka da aiki Maigida.” Na gaishe shi a dai dai lokacin da na karasa wajensa. Na leka cikin injin ladar.
“Barka kadai.” Ya amsa ba tare da ya dago kai ya dube ni ba. Ya samu rabin minti yana aiki bai dago kai ya dube ni ba, sannan ya dan juyo. Da ya ganni a cikin kayan gida sai kamaninsa suka sauya.
“Lafiya dai ince ko?” ya tambaye ni. Na ce lafiya kalau. “To yaya na ga haka? Ka makara amma kake bata lokaci. 'Ya dubeni sosai da ruwan kasar idanunsa sannan ya ce “Dahiru 'yan kwanakin nan ban san abin dake damunka ba. Baka son aiki ko kadan. Bayan shekaru biyu baya ban sanka da lalaci ba amma duk ka sauya. In ce ko ba shawarar Bimo kake dauka ba.”
Na ce. “Ko daya babu wata shawara da Bimo ya ke bani. Bana jin dadin jikina ne kurum tun daga lokacin da aka taso mu daga titin jami'ar Bayero.”
“To mene ne ke damunka, mutuwar zuciya."
Na yi ajiyar zuciya. Sannan na sunkuyar da kaina. Don bani da abin cewa. Da ya ji ban ce komai ba sai ya ci gaba. “Dahiru gaskiya zan gaya maka in ba zaka zage ka yi aiki ba to zamu rabu.
“Ba wai ina nufin na kore ka ba, saboda mun dade tare da kai na kuma san matsayin da kake na maraici, amma bana son lalaci. Na san yanzu kasuwa ta lafa mana tun tasowarmu daga titin Bayero. Saboda haka ya kamata ka lura ka gane a matsayin da nake ciki. babu ciniki, amma wannan bai hana ni baka abin da na saba baka ba, ka san a maimakon abin da nake baka ba wani abu nake so ba face aiki tukuru.”
Ya sunkuya ya dauki sufana da ke yashe a kasa a gabansa. “Bimo kanina ne, amma saboda rashin aikinsa da yawan makararsa dole ne mu rabu, nan ba da dadewa ba, saboda haka ka mayar da hankali, na kara jaddada maka ka mayar da hankali ga aikin nan, don kuwa da aikinka na dogara. Ya kamata mu sake fito da sunan garejin nan” Ya koma ga aikinsa. “Jeka ka shirya ka fito aiki.”....
DOMIN CIGABA DA KARANTAWA SAI KU SIYA LITTAFIN AKAN 200 A OKADABOOKS TA HANYAR DANNA MABALLIN PURCHASE AT OKADABOOKS DAKE ANAN KASA
PURCHASE @ OKADABOOKS
DOWNLOAD NOW