Daga Taimako; littafin gwarzuwar marubuciya SADNAF
Littafin yana wa'azantarwa ne akan wulakanta mutane gamida sanin darajar dan Adam da mutum ta shi
Hakanan littafin ya tabo bangaren nishadi yadda marubuxiyar tayi amfani da kwarewa ta wurin sakala cunkun nishadi wanda ko tantama banayi muddin ka karanta ko kika karanta littafinnan tofa sai kun dara
To kada dai na cika ku da surutu ga kadan daga cikin littafin
Wata matashiyar buduruwa na hango a zaune akan tabarma,tana ta guga,dagani kayan mijinta take gogewa Muhibba kenan,wacce bata fi wata Biyar da aure ba,gidanta madaidaicin gida ne,dan wanda take aure ba mai k'arfi bane,Palo d'aya ne da d'akuna biyu,sai kitchen da toilet,Mijinta Abdulmajeed Mallamin Makarantar primary school ne,dai dai gwargwado suna cikin rufin asirin Allah,auren soyayya suka yi,Muhibba tana da kirki sosai ga kyauta,tsafta awajenta ba a magana,Dan inka shiga gidanta kamar karka fito sabida kamshi da tsafta da gidanta ke dashi,kayan mijinta data wanke take gogewa taji ana kwankwasa gidan,d'aga murya tayi tace "Waye"? Ji tayi an k'ara kwankwasa wa batare da anyi magana ba,mik'ewa tayi ta nufi k'ofar Dan taga wa ke kwankwasawa,doguwar Riga ce a jikinta tayi parking ba dankwalli akanta,daga bayan k'ofar ta Dan tsaya ta bud'e k'ofar tana leko da kai Dan taga waye, wani irin fad'uwa gabanta yayi jikinta ya d'au rawa sakamakon tozali da tayi da wata farar mata mai tsayi,idonta manya manya girmansu ya wuce misali,tsayinta ma yayi yawa, farinta wani irin d'aukar ido ya ringayi,gashin girar ta jajaye,haka ma leb'enta,murmushi wanan matar tayi mata tace"kiyi hakuri na zo na takuraki da kwankwasa k'ofa Dan Allah fitsari ne ya matseni shine nakeso ki taimaka min inyi dan bansan kowa anan ba," Muhibba tunda tafara magana gabanta ya tsananta fad'uwa ta kuma kasa addu'a dan matar yanayinta abar tsoro,Dan zata iya cewa tunda take ba ta tab'a ganin mai irin tsayinta ba,d'aurewa tayi tace cikin rawar baki " lah bakomai shigo kiyi" da sauri matar ta shiga ciki,ta tsaya atsakar gida,Muhibba kuwa kamar tabar gidan da gudu Dan wani irin tsoro ne ya rufeta,gashi tana so tayi addua ta kasa,d'aurewa tayi ta shiga tayi hanyar da band'akin yake tace mata "bismillah ga band'akin akwai ruwa aciki" gani tayi matar ta nufo ta kamar ba tafiya take ba turota ake, ware ido tayi tana kallonta cikin tsananin tsoro da tashin hankali,dasauri tabi k'afarta da kallo taga babu alamar k'afa illa ma doguwar Riga dake jikinta kawai dake Jan kasa,jikinta ne ya d'au rawa kafin tayi yunkurin yin wani Abu wuf matar ta shige band'aki ta rufo k'ofar,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun" muhibba tace cikin tsananin tsoro da fad'uwar gaba hanyar waje tayi da sauri taje ta tsaya daga bakin k'ofar tana kallon band'akin shiru shiru matan nan bata fito ba,tsoro ne ya k'ara rufe Muhibba ta d'aga murya tace " Baiwar Allah har yanzu baki gama ba" shiru taji,ba ayi magana ba,hakan ne yasa tayi waje da gudu ta nufi gidan dake kallon gidanta,gidan surayya makociyarta ce suna mutunci sosai da ita,bubuga gidan taringayi da sauri tana kallon gidanta,Surayya kin bud'e k'ofar tayi sai data ce "Muhibba kin tabbata kece"? " nice mana yi sauri ki bud'e min"bud'ewa Surayya tayi ahankali ta leko da kanta itama kana ganinta kasan a firgice take,da sauri Muhibba ta shige kafin tayi magana surayya tace " kema kinganta ko" ? Cikin tsananin tsoro Muhibba tace wacece"? Cikin sauri tace " bakiga wata farar mata mai kama da aljana ba,gidan nan tazo wai na taimaka mata fitsari takeji tuni na rufo k'ofata dan wlh baki ganta ba kamar ba mutum ba" tunda surayya tafara magana jikin Muhibba yafara rawa gabanta in banda fad'uwa babu abinda yakeyi d'aurewa tayi tace " Innalillahi wa inna ilahi rajiun Surayya na shiga uku na lalace,wlh tazo gidana tunda ta shiga band'aki taki fitowa har yanzu, nashiga ukuna D🅰G🅰 T🅰IM🅰KO zan janyo wa kaina balai Dan Allah zoki rakani inga mai take yi a band'aki tunda zu,Wani irin tsalle surayya ta buga tayi gefe tace " wa tab bazan iya rakaki ba,wane tsautsayine ya kai ki kika barta ta shigar miki gida,wlh wanan da gani ba mutum bace Aljana ce," ai tun kafin Surayya ta rufe bakinta,Muhibba ta d'ora hannu aka taringa kuka tana ta shiga uku ta lalace " Yanzu surayya ya zanyi wlh tana cikin band'aki har yanzu bata fito ba," sallati Surayya tayi tasa hijabinta tace "muje in rakaki Allah yasa ba aljana bace.
TOH DOMIN KARANTA CIKAKKEN LITTAFIN SAI KU DOWNLOADING NASHI A NAN KASA
👇👇👇👇👇👇👇👇👇
DOWNLOAD NOW
PURCHASE AT OKADABOOKS
DOWNLOAD PDF
DOWNLOAD DOC
DOWNLOAD TXT