GOBE JAR KASA
Littafin fasihi kuma hazikin marubuci shafi'u Dauda giwa
Littafin ya magantu ne akan wasu gwalagwalai da wani rikakken barawo ya sata ya boye babu yadda yansanda basuyi da shi ba don ya fada masu inda ya boye gwala gwalan amma na tsohon mai suna NALAMMA yaja tunga ya kafe yaki fadin inda ya boyesu,
Bayan shekaru da dama a lokacin an tura nalamma gidan jarun, harya tsufa acan rannan sai rashin lafiya ta kamashi akai maza aka garzaya asibitin cikin gari da shi
To anan nefa wasu rundunar yan fashi sukai muguwar artabo da yansanda kana suka karbi tsoho nalamma don ya fadi masu inda ya boye gwalagwalen daya sata ahekarun baya,
Shiko tsoho nalamma yaki fadamasu to ashe dai lokacin da aka kwantar da nalamma a sibiti yafadi wa wata nurse inda gwala gwalen suke ita kuma ta dau saurayinta mai suna nura suka nufi wurin bayan sun samu gwala gwalan ne NUra yai niyyar kashe budurwartasa inda ya bita da diga yana kokarin buga mata duk dan ya mallake dukiyar gaba daya.
Wayannan gwala gwalai sunyi sanadiyar MUTUWAR mutane da dama, sun shiga hannun mahandama da dama kuma sun fita,sun shiga hannun maciya amana da dama kuma sun fita,,,
Shin au waye zasu samu nasaran mallakar gwala gwalan nan
Wannan amsa zaku jita ne a cikin littafin nan mai suna GOBE JAR KASA
Sai ku downloading littafin a nan kasa