BIRNIN AZZALUMAI
Kashi na shida 6
Complete ebook PDF
Wannan shafi tamu mai Albarka kwanakin baya ta fara kawo maku wannan littafi tun daga kan na dayansa har zuwa na biyar to da yardan Allah ayau mun kawo maku na karshe Wanda shine karshen LITTAFIN Baki daya
Littafin BIRNIN AZZALUMAI na Abdulaziz sani m gini
Kadan daga
A sannan alkalin gasar ya shigo ya tsaya a tsakiyarsu ya
dadda tuna musu yanayin gasar da kuma dokokinsa..
Daga cikin dokar gasar shi ne in dai mutum ya fadi kasa
da bayansa babu damar a sake kai masa wani hari ko a
cutar dashi sannan kuma a cikin jaruman hudu duk irib
yanayin daza su shiga wani bazai taimaki wani ba kuma
duk wanda ya mutu a wannan gasa babu batun daukarr
fansa sbda dama gasa ce mai hadari ta sai da rai.
Alkalin yana gama yin wannan jawabin sai ya fice daga
cikin filin ya koma cikin yan kallo yana zauna daf da
jarumi zaunal.
Faruwar hakan ke wuya aka buga gangar fara gasa.
Nan take sai jaruman hudu suka ja baya kuma kowannen
su ya murtuke fuskasa alamar cewa ba sani ba sabo
kuma ba ragayya..
Kamar hadin baki sai dukkaninsu suka zare makamansu..
Husam da lasmir suna rike da takubbansu da
garkuwoyinsu, sarki zarmus da gimbiya zarisha kuwa
suna rike da takubba guda bibiyu.
Bayan jaruman hudu sun ja baya ga juna sai suka fara
kallon kalo kowannen su na nazarin abokin gwaminsa har
izuwa tsawon yan dakiku daga can kuma sai suka rugo da
gudu izuwa kan juna.
Zarisha ta afkawa lasmir shi kuma sarki zarmus ya
afakawa Husam aka ruguntsume da azabbben fada ya
zamana cewa suna kai wa junansu sara da suka cikin
tsananin zafin nama tunga da jarumtaka.
Page 5.
Zidane kd.
Duk sa adda makamansu suka hadu sai dai kaji kara da
tartsatsin wuta na tashi.
Nan fa filin ya rude da shewar jama a .
Sai da jaruman hudu suka shafe kusan dakika dubu daya
da dari uku suna fafata azababben yaki batare da
dayansu ya sami nasarar koda kwarzana a jikin daya ba.
Babban abin da ya fi daurewa mutane kai shine duk salon
da sarki zarmus suka zo shi sai a gasu zarisha ma sun iya
hakama lasmir duk salon dasuka zo shi sai aga cewa sun
hasam sun iya..
Koda jaruman hudu suka ga sun shafe wannan tsawon
lokaci suna gurmurzu ba tare da sun sami wata nasara ba
sai duk suka ja da baya.