BAKANDAMIYAR GUMURZU
Kashi na biyar 5
Na Umar Abdulhadi mati
DOMIN DOWNLOADING LITTAFIN ZUWA KAN WAYOYINKU SAI KU DANNA KASANNAN 👇👇👇👇👇👇👇
[post_ads]
Cikin murya mai amo sarki alkasim ya cigaba da magana haƙiƙa ka ha'incemu, ka yaudaremu kuma kacika hatsabibi a duniyar tsatsuba tunda hsr ka iya ɓoyewa mudubban tsafinmu al'amuranka duk da cewa kowannenmu ya takawa matsayin da saidai Allah ya isa a duniyar tsatsuba, haƙiƙa ka kayi wasa da hankalinmu tunda har kake ƙoƙarin anfani damu wajan cikar burinka a gefe ɗaya kuma kabarwa kanaka abin kunya tunda bazaka iya fita kayi karo da maza ba domin cikar burinka kamar yadda kowani sarki mai cikakken iko da tsatsagoron jarumta da bajin yakeyiba sai ka ɓullo ta hanyar yaudara da zamba haƙiƙa ka ɓallowa kanka aikin da zaiyi sanadiyyar tarwatsewar birninka, natsani yaudara da mayaudari bana zamba domin wanan hallayace ta mutanen dake da rauni dan haka, hm dandai ba'a ƙwacewa yaro galma, idan yaro yace zai haɗiye gatari ai sai a sakar masa ƙota dan haka wanan yaƙi bai shafeniba amma acikinku kai da aljani duk wanda yace zai taɓa jama'ata ko zai shiga gabana ina rantsuwa da izzata da buyar mulkina sai na kawar dashi a yanzu zan ɗauki mutanena mu bar maka ƙasarka yana zuwa nan a zancen sai ya tafa hannunsa yin hakan ke dauya sai wani farin hayaƙi ya zagayeshi shida tsirarrun dakarun dake tare dashi hayakin na yayewa aka nemesu aka rasa kamar basu taɓa bayyanaba, ganin haka yasa sarki laffaru, sarki mahraz, da sarki dujalu, shamharu, da sauran sarakunan da suka halarci wanan gasa da hamshaƙan matsafa da sauran shahararrun jarumai wanda suka halarci wanan gasa suka fara haɗa kayansu suna fita daga filin gasar kada shafi ta shafesu cikin sa'oi kaɗan filin gasar ya rore yakasance sauran kusan rabin mutanen da suka halarci wanan gasa sun fita daga filin sun kama gabansu.
Mafiya yawan waÉ—an da suka rage sun fito ne daga jinsin dodanni da aljannu waÉ—anda suka rage nadaga jinsin mutane sune mutanen birnin ruma wanda bazasu iya tafiya subar sarkinsu ba.
Hakan na faruwa sai sarki nawwar ya tafa hannayensa kamar wasa sai ƙaran tafi ya fara fitar da amo mai ƙarfi wanda ya karaɗe dukkan filin gasar kai shadama cikin birnin ruma da ƙauyikan dake zagaye dashi, duk ɗan asalin birnin ruman da yaji wanan ƙara nan take zai miƙe cikin kaɗuwa da gaggawa ya fara shirin yaƙi domin wanan alamace daga sarkinsu mai nuni da cewa gari ba lafiya an kawo musu hari kafin kace kwabo tuni jarumai maza da mata sun fara ɓuɓɓugowa daga dukkan birane da ƙauyikan dake zagaye da birnin ruma suna masu tunkarar wanan fili na gasa....
DOMIN CIGABA DA KARANTAWA SAI KU DANNA KASANNAN 👇👇👇👇👇
[post_ads]
[post_ads]
ga duk wayanda suke samun matsala ta wurin downloading ebooks namu kuma suke da bukatar mu rubuta masu copy din littafin mu turo masu ta whatssap ko profile nasu
SAI KU TUNTUBI mamallakin shafin Shuraih
Usman
Ta facebook profile nashi
Kota nambar waya 08140419490
Kota adireshin Email
shuraihusman@gmail.com
Sai de ku sani wa hakan zamu cajeku wasu kananan kudade
its Shuraih U sman 99%