ABADAN
littafin Safiyya Abdullahi Huguma
KADAN DAGA CIKI
[post_ads]
sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar mai tausayin qasa,a zahirance idan ka
ganta sai kayi tsammanin ranar bata dameta ba saboda yanayin yadda take
tafiya,saidai sam tana daga cikin wadanda rabar ma tafi gallaba,don har Allah
Allah take taga ta isa gidansu,saboda leshin dake jikinta dinkin riga da skert da
kuma dogon hijabinta mai hannu dake qara mata zafi wanda ya zamo too match ne
da kaya jaka da 'yar jakar swagger dake maqale a kafadarta
babu wata doguwar tafiya ta iso qofar gidan nasu wanda ke rukunin gidajen marasa
wadata,duk da ginin bulo da bulo ne saidai bai samu arziqin fulasta ba bare a kai ga
fenti,ta cire jakar kafadarta tana shirin shiga soron gidan idanunta ya sauka kan
hauwa wadda ta cakare cikin kwalliyar atamfa,wani matashin saurayi ke fiskantarta
wadda yanayin tsaiwar tasu kawai zai fahimtar da kai zance suke,dauke kanta tayi
tamkar bata gansu ba don wannan dabi'a ta hauwan bama ita ba duka yaran gidan
na bata haushi
ta tsakiyarsu ta raba zata wuce kasancewar babu wata hanya sai ita taji saurayin na
fadin‘’barka da dawowa antyn mu‘’
‘’yauwa sannunku‘’ta amsa masa ba yabo ba fallasa tare da shigewa cikin gidan
hauwa dake binta da harara kamar qwayar idonta zai fado ta ja wani matsiyacin
tsaki
''gaskiya haruna kana bada ni wallahi,wai ksi me yasa kullum baka da,burin da ya
wuce ka yarfani a gun wannan matar ne,me ma kake nufi ne ni fa ban gane ba''
''yanzu laifi ne kulu don na gaisheda yayarki,kuma fa kin sani tana da kirki
wlh,uwa uba ilimi da nutsuwa''
cike da masifa hauwa ta qwalalo ido
''iyeee,to ko zaka koma gurinta ne haruna,a gabana zaka dinga yaba wata uwar
mata da ta shekare gaban iyaye aka rasa mai dauka?''
ganin hauwan ta hau da yawa yasa ya sassauto''haba kulu na,wata kai yake a gurina
ai kema kin sani,ni mai zanyi da wata mace a duniya indai ba ke ba?''
duk da koda tan da yayi ta dade a kumbure kafin ta sauko ta yarda suci gaba da
tadinsu
sallama tayi tsakar gidan kamar yadda ta saba duk da ta san babu mai amsa mata
matuqar ba mamanta bace a tsakar gidan ko hindatu,ile kuwa bata samu kallon
arziqi ba bare na tsiya duk da inna hadiza dake zaune gabas da tsakar gidan nasu
tana kasa wake da shinkafar siyarwarta cikin samirun da duka suka sha
lamba,zaune kusa da ita kuma huwaila ce ke nata zarafin na qulla kunun tsamiya
cikin farar leda tana lodawa a botiki
bata fasa ce musu sannunku ba kamar yadda basu fasa ja mata tsaki ba tare da binta
da harara har ta cire toms dinta ta kwashesu a hannunta don gudun samun sabani ta
shige rumfar mahaifiyarsu ba da sallama,tana iya jiyosu sun fara sana'ar tasu wato
yada habaici da baqaqen maganganu
''hmmm idan da ranka kasha kallo,kaje ka gama yawon dandinka ka dawo dakin
uwa kayi zamanka''
''kema huwaila idan banda abinki a banza suka qi aurar da ita?ba ana fasa musu
kai da cewar kyakkya wa,bace 'yarsu?,ai dole su maisheta jari''
''hmmm,Allah wadaran naka ya lalace kuwa,wataran kuwa za'a dire abun kunya
cikin gidan nan,a juri,zuwa rafi da tulu debo ruwa''
duk sunajin abunda suke fada daga ita har maman tata,wanda idan da sabo tuni sun
saba,saidai babu mai tanka musu,kan dadduma ta taradda maman tata,da alamu
sallar azahar take abatarwa,saboda haka ta sabule jakarta ta ajjiyeta saman kujera
hade da hijabinta ta sake yowa tsakar gida don,dauro alwala,har ta gama,alwalar
tata basu fasa muna nan maganganganunsu ba,babu wadda ta daga kai ta kalla a
cikinsu duk da irin suyar da zuciyrta ke mata da radadi,ta ajjiye,silifas,din da ta
daura alwalar tana niyyar shigewa rumfar tasu
isyaku dan wajen inna,hadiza ya tawo a guje hannunsa dauke,da kwanonsha cike
da kunu,bata ankara ba taji shi yana bin skert dinta ziwa qafafunta,da,sauri ta kalli
yaron dake tsaye qerere ya zuba mata ido tace''haba isyaku me yasa baku iya tafiya
ne a hankali?''
baki ya murguda ya galla mata harara
''eh din,ba sai a koya min ba,ban iya ba,aikin banza taqi aure ta damu mutane cikin
gida''
ranta ne yayi masifar baci,yaron da a qalla ta bashi shekaru kusan goma sha biyar
shi zai tsaya a gabanta yana gaya mata haka,hannunshi ta,finciko ya qaraso
gabanta,kafin ta aiwatar da komai ta jiyo muryar inna hadiza cikin kaushi da haya
gaga tana fadin
''ke,kada ki kuskura ki taba min yaro wallahi,idan kuwa kika sake hannunki ya kai
kanshi to zamu kwashi 'yan kallo dake wallahi''
bata saurari kurarinta ba ta yarfawa isyaku mari domin dama ko da,safe kafin ta
fita sai da ya mata wata tijarar kuma tana kallo bata ce uffan ba sai dariya ma data
sheqe da ita ,ai kuwa kanta tayo yana fadin
''kutumar uba,wallahi yau sai kin gane shayi ruwa ne''
gadan gadan ta nufota wand hakan yayi daidai da shigowar malam mamuda cikin
gidan
''kai kai lafiya?''
''yauwa malam gwara da Allah ya kawoka,wallahi mun gaji da zaman wannan
balagaggiyar tsakaninmu,ita ba aure ba ita ba karuwanci ba,ta ishemu ta ishi
yarranmu?''ya katseta da fadin
''to yanzu me kuma ya faru?''
''wai wannan dan talilin yaro ta daddage ta zabgawa mari don kawai ya zuba mata
kunu bai sanig bau,to wallahi ba zan yarda ba,ko ya rama ko ni na rama masa da
kaina''
''kai isyaku me yasa haka''
''baba ban sani bane ba fa,kuma ni wallahi sai na rama''
''ke *maryam* bashi haquri''
babu yadda ta iya haka tace kayi haquri
shi kuma ya tubure ramawa zaiyi,da qyar uwar tasa ta lallabashi ya haqura
hawaye na bin kuncinta ta shige dakin nasu,maman na zaune bisa daddumar yadda
ta barta ko motsawa bata yi ba bare tasa baki a cecekucen da akeyi,bata ce da
maryam din uffan ba kamar yadda itama batace din ba,ta dauki dadduma guda
daya daga inda suke ajjiyewa ta tayar da sallah
ta dade akai tana miqawa Allah kukanta kafin ta sallame,tana ninke sallayar ne taji
maman tace
''na sha gaya miki maryam dole kici gaba da haquri matuqar dai kina zaune ne
cikin gidan nan''wasu sabbabbin hawayen ne suka zubo mata,ta koma gefan daya
daga cikin kujerun falon ta zauna tana fadin
''mama,ke kanki shaida ce akaina,amma duk yadda kakai ga haqiri wataran
mutanen gidan nan sai sun saka kayi misbehaving,yanzu mama kamar isyaku fa
qanin bayana mama?''
''ya isa kada ki saka abun cikin ranki,Allah yana tare dake ba wai ya manta da ke
bane''
cikin sanyi wanda ya zamto halittarta ta goge fuskar tata cike da tawakkali da miqa
lamuranta ga Allah
''to mama''shine abunda ta fada a sanyaye
DOMIN CIGABA DA KARANTA SAI KU DOWNLOAD NA LITTAFIN A NAN KASA 👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇
[post_ads]