HIKAYAR BIRNIN DUWATSU part 2 hausa Novels Audio
Cigaban labarin Abdullahi dan falilu da ƴan uwansa
via https://youtu.be/f0fiIhyybHE
Cigaban labarin Abdullahi dan falilu da ƴan uwansa
via https://youtu.be/f0fiIhyybHE
TASKAR AJALI Littafi na daya 1 complet Audio
Munfara sabon littafi jama'a ayi mana hakuri na jinmu da akayi shiru na yan wasu kwanaki in Allah yayarda mun kusan dawowa kan aiki
via https://youtu.be/O915k1cbv9g
Munfara sabon littafi jama'a ayi mana hakuri na jinmu da akayi shiru na yan wasu kwanaki in Allah yayarda mun kusan dawowa kan aiki
via https://youtu.be/O915k1cbv9g
BANGON DUNIYA PART 1E} Jiragen ruwa sukamike acikin Bahar xum sai tafiyasuke maxaje na rafka ihu gamida kururuwa suna saran,iska da takobi basuda wani buri face Fatan aukuwar bala,i suna sha,awar xubarda jini dagwada karfin dantse ga abokaningaba dayake tafiyace da akeyinta bisa alkaluman tsafi tuni sun tsallake Bahar Xumsunfada Tekun Xurum ai tafiya kandan sukayi sai akaji Sarki Kaushatu dan Kan,ana jikan Kurungu mugun kifi kada naganinka yakwana da yunwa yadaddage yakwarara ihuyanacewa kai maxaje matuka jiragen ruwa daga jinsin aljannu da mutane mudafe datuki domin Gakifi Kurdum can agabammu kuma haryanxu Sarkan ajalina taredashi tananan acikinsa take Dakaru sukaiduba gabansu kawai sai sukahango ruwa nawani toroko yanaxillo yanakara gaba da sauri alamun tafiyarKifi Kurdum maxaje sukasa ihu dakururuwa sutunkari wannan Kifi Abinka da harkan tsafi tuni Sucimma kifi sukewayeshi babu hanyarda xai iya guduwa kifin yabayyana asaman ruwa girma kifi yayigirman Giwa girmansa yawuce misali domin ganin girman kifinkawai ya,isa yasa Xuciyar maxaje tabuga abinkada shu,umim kifi sai yarika kallon maxaje daya bayandaya kamar yana irgasu Sarki Kaushatu yakwarma ihu yace kaiKifi Kurdum lallai abisa umurnina inacewa ka amayoda sarkan daka hadiya mutukar kana bukatan kacigabada rayuwa cinkin Salama Kifin yai gunji kawai sai yanutse cikin ruwa nanfa dakarun Sarki Kaushatu sukama dawur dawur da idanu Sarki Kaushatu yace maxaje lallai kukasance cikin shiri domin komai xai iya faruwa,lallai dayuwam xa,amutu kwatsamsai Kifi Kurdum yayo sama yafuto daga cikin ruwa asamansa akwai tsinannun aljannunnan guda bakwai masu sarrafashi suna rike dawasu bakada kwari dankari aisai suka fara sakin kibau gadakarun sarki Kaushatu dan Kan,ana Kamar saukan ruwan sama nanfa sushiga babbakealjannuda mutane ihun maxaje yagauraye ko,ina aljannunnan bakwai surikita Jama,ar sarki Kaushatu kisa suke bashara,a nanfa masifa tasamu gindin xama wutar yaki taruru mutuwa tarika shawagi akammaxaje tana wafce rayukansu tana watsasu kiyama tsabar masifa na aljannunnan bakwai sai sudaka tsallesubar kan kifin sudira ajiragen ruwan dakarun Sarki Kaushatu sufarma maxajeda sara dasuka sutarwatsa jirgi sukashe jama,ar ciki subankama jirgin wuta yakone kurmus shikansa Kifi Kurdum saboda Shu,u,manci tako,ina feshin wuta yakeyi bakida hancinsa da fuka fukansa yana kone abokan gaba kaiya aikoda Sarki Kausatu yaga balbalin bala,i damasifa da ake saukema dakarunsa sai yakwarma ihu maitsananin kara da rudarwa yaxare takobi yai girgixa take yarabu xuwa gida bakwai kowani daya yafuskanci aljani guda dankari nanfa yaki yasauya salo domin wata sabuwar masiface akwantota tsakanin aljannunnan da Sarki Kausatu yaki yasarke maitada hankali Tuni yasa gatari alokaciguda yafaskara kan aljannu uku yafasa kijin biyu yamurde wuyan daya kawai sai ragowan aljaninnan yabace ajikin Kifi Kurdum sannan kifin yatashi Sama daniyyar guduwa Sarki Kaushatu yahade guri daya yai girgixa yatashi saman yariski katon kifinnan sukacame da yaki asama shida kifinnan kayya lallai wata tsiyasai dangado koda masifatai masifa sai sukarika sakema juna bala,i,daga kofofin tsafi tuni suka haifar dawani hayaki gamida rugugi maitada hankali kifi Kurdum yabusama Sarki Kaushatu wata Shu,uman wuta takama ilahirin jikinsa bakidaya hankalin jama,arsa yatashi shikuma kifinnan sai yatsaya asararin samaniya yana wani juyi kamar yana wasan Farinciki kayya da kifinnan yasan masifar da xata sameshi da yakara gaba aguje domin lokaci daya wutar tamutu sai SarkiKaushatu yabayyana yaya wani baki sannan yakunbura yakara girmatsanani girama yaninka kifinnan biyu yakwarara ihu yamika hannunsa tadanki Kifinnan yakafa hanna yensa abakin Kifin kamar Gora haka Sarki Kaushatu yabara kifinnan gida biyu yai jifada sassan jikin kifinSai Sarkan ajalii tabayyana asama Sarki Kaushatu yakaimata kamu amma shu,umar Sarkan saita xille tayo kasa xata fada cikin ruwan tekum Xurum Sarki Kaushatu yabiyota da tsananin gudu yana kwarma ihu yanacema dakarunsa kucafeta kada kubarri ta afka ruwannan aisai aljannu da mutane sukai cincirundo suka daga hannayensu domincafe sarkannan shikuma Sarki Kaushatu sai yarika saukowa ahankali domin yasadakar cewa Bamakawa Dole Sarka ajali tasauka ahannun daya daga cikin Dakarunsa kawai sai yarika kyakyata dariya abinsa Kayya da Sarki Kaushatu da jama,arsa sunsan masifarda xata afkamusu toda kowa yai takansa domin lokacinda Sarkar tayo kasa taxo dabda Dakarun Sarki Kaushatu Sai tafudda wani masifaffen haske haske yaketa tacikin dakarun Sarki Kaushatu abin bakyan gani domin haka hasken yarika shiga jikin aljannuda mutane yanafasasu kama tangaran haka suke tarwatsewa wohohonanfa tekun yarikede yaxama tekun jine yacika da gawawwakin aljannu da mutane, Sarkan tatsundumacikin ruwa Sarki Kaushatu yakwarara ihu shima yatsunduma cikin ruwan yakunna nutsu inda yabar dakarunsa suna cigaba da fashewa can yafuto yatsaya asaman ruwa yakama karanto kalaman tsafi gamidasuburbudo warkoki daga Warkokintsafi saiwani janhaske yashigi jama,arsa take sudaina fashewa alokaci guda kuma ruwa tekun yakafe halittun ruwan suka bayya afili tsananin Fushi sai Sarki Kaushatu yabusa musu wutar tsafi yakonesu bakidaya shida Jama,arsa suka koma kan tudu yakalle dakarunsa wanda adasunkai miliyan bakwai amma yanxu basuwuce miliya ukuba yakwarma ihu yace ahalin yanxu Sarka ajali tabar cikinruwa kuma wata Matsafiyar aljana maisuna Jajira itace tawufce sarkan Yadagamurya yacekuma tadauki ajalinta kawaisai yaigudu maxaje rufamar baya INASUNUFANE SHAYI YA ISO
#BANGON DUNIYA PART 1 G
Lokacin da Sarki Kaushatu yakumbura kuma ya harxuka yakwarara ihu sai ya afkama Macijiya Dallura da wani irin yaki maitada hankaili itama ta ruftamar sushiga farautan ran juna amma awannan karan labari yasha banban domin tuni Sarki Kaushatu yama Dallura raunika fiyeda Sittin yasare mata kawuna biyar inda yatasata agaba yana sauke mata axabar yaki dakanta taja baya sannan ta xubbda makamanta tai sujjada ga Sarki Kaushatu tace daga yau nibaiwarkace domin kai shaidanine uban Shaidanu Sarki Kaushatu yakeceda dariya akarke yakwarara ihu yace wane yaro kuma wane uban yaro ni Sarki Kaushatu dan kan,ana jikan Sarki Kurungu tsinanne uban mutsiyata Yadubi jama,arsa yace kowa yashirya xamu tunkari Dutsan wuta domin acanne Aljana Jajira take Rayuwa ahalin yanxu ta ajiye Sarkan ajali atsakiyar Fadanta sannan takewaye ilahirin dajin da shaidanun aljannu masu mutukar hadari lallai su iblisaine wadanda atarihinsu basusan faduwaba balle tsoro sukashe mutum kuma sunacin naman mutu haka kuma suna kashe aljani kuma sunacin naman aljani tabbas mudasu xamu gwabxa yaki mai take sai mai tsawon kwana kawai sai yadaka tsalle yahaye dokinsa yasaki Linxamin doki yanna cikin Dokar daji bakida dakarunsa suka rufamar baya hada maciya Dallura saida sukai tafiyar wata guda cur bisa alkaluman tsafi Sannan Suka isa Dutsan wuta wani kasur gumin Dutsene da yaxagaye dajin kaf babu wata hanyar wucewa sannan da xaran katunkareshi to xaima feshin wuta kakone kurmus dankari koda suka iso wannan waje sai suka tsaya inda Jama,ar aljannu da mutane gamida Dodanni suka tsorata daganin wannan Shu,umin Dutse domin aman wuta yakeyi bakakkautawa babu wata hanyar wucewa Sarki Kaushatu dankan ana yakarema Dutsannan kallo tsaf sannan yadubi jama,arsa yace yaku jama,ata lallai kusani bamuda wata hanya face muketa tacikin wannan gagarumar wuta mu haura dutsannan muriski aljana Jajira domin fadarta nabayan wannan tsinannen Dutse ai sai Hankalin jama,a yatashi domin kowa yasan shiga wannan wuta tamkar sallamama Mutuwace Koda sarki Kausahatu yafahimci Jama,arsa suntsorata ainun sai yabushe dadariya inda akarke yakwarara ihu sannan yaxarce takaranto wasu kaman tsafi yanuna wutarnan dankari ai amaimakon wutar ta mutu sai akwarara ihu wutar takara toroko tai Sama tashiga feshi tanayin harshe tana laso jama,ar aljannu da mutane daga rundunan Sarki Kaushatu tana kone su tuni jama,a Sukaja baya ran Sarki Kaushatu Yabaci yatunkari Wutar yanarike da wani bakin mashi da bakin Garkuwa tabbas iblishi iblishine domin tilas Wuta tadaina feshi takoma gudaya tairmi tanaci balbal Sarki Kausatu yaci gabada kusantar Wuta sai akara kwatsatsa ihu anacewa kai tsinanne lallai yauce ranan mutuwarka kawai Sai wasu jajayan Gwaggo birai girmansu yakai girman katuwar bishiyan kuka jajur suke kamar Garwashin wuta jikinsu harcida wuta yakeyi suka rika futowadaga cikin wutannan suna rikeda takubba yawansu yaxarce misali muninsu baxai fasaltuba suka afkama Sarki Kaushatu dayaki irinna amatu ko airai nanshima yafada musu sushiga gogawa dankari yaki yakaure inda sukarikaimai sara da suka yanakarewa gamida gocewa yana maida musu da martani wani abin takaici shine kwata kwata makami baya tasiri ajikinsu hankalin Sarki Kaushatu yatashi yafusata yarafka ihu yadaga hannayansa sama yarintse idanunsa yana karanto karatun Sur kulle inda biroyinnan suka rika tafkamar Sara dasuka amma kamar suna saran Dutse sambaidamu da suba takubbasu suka rika kararayewa can amaka wata tsawa da walkiya mai tsoratarwa dankari jama,asuka furgita anemi Sarki Kaushatu arasa yabace bat nanfa Dadakarusa da abokan artabusa sushiga xare,idanu amma bashi ba alamansa can akwarara tsawa gamida walkiya jama, sukadaga kai sama,atsorace kayya tsinanne tsinanne ai saiga Sarki Kaushatu na saukowa daga sararin Samaniya yana cikin wata damaran yaki jakur yanarike dasu jajayan gatura wata naci ajikinsa balbal kai inka ganshi saikadauka Iblishin Tabdijama ai Saikallo yakoma Sama domin al,amari yaxama masifa dabala i sannu ahankali yadira akasa kasa tai girgixa duwatsu suka ammsa koramu sukama ammbaliya dawakai suka xarya suna neman shiga dajiiiAmma gwaggwannin biriroyinnan sai suka jadaga dashiri Gumu KAI WANNAN SHAIDANINE NANUFI RUMFARDHAYI ABOKAI
{#BANGON DUNIYA PART 1 {-I~}Lokacinda Sarki Kaushatu dan,Kan,ana Tunku maikai yaro makasa yadira akasa saida hankalin kowa yatashi domin tunikasa takama girgixa koramu sukama ambaliya hankalin Halittun daji manya dakanana yatashi sukama xarya acikin daji sarki Kaushatu yakwarara ihu yajijjiga gaturan hannayansa yadubi Makamakan gwaggon birannan yace kai tsinannu ganinan gareku yafalfala aguje yatunkaresu suma sukwarma ihu sutunkaroshi ahassale suka hadu atsakiya akai kwaram kwatsam dankari ainan halittunnan suga balbalin bala,i da masifa domin wani,irin kisan gilla yakemusu tamkarbarnan iska haka yake fatalidasu tamkar guguwar annoba haka yake turasu kiyama duk inda yakutsa sai kaga gawawwaki naxuba kawuna natashi sama yasare yabanke gamida Farkewa dankari koda masifataimasifa halittunnan suji masifa aisai suka tarwatse amma saboda bala,i irinna Sarki Kaushatu sai yakwarara ihu tuni watamasifaffiyar wuta tabisu daya bayan daya takonesu kaf Sai yajuya yaceda jama,arsa kubiyoni mutnkari tsinanniya Jajira take yanufi Wutan yana wanidam dam yanaham aisai wutan tarabu biyu hanya tasamu kai tsaye sarki Kaushatu yafada hanyar shida Jamarsa sukawuce lami lafiya sannan suka riski katom dutsennan mai aman wuta dankari babu wata hanyada xasu wuce face wutarnan tababbakesu nanfa akai cirko cirko Sarki Kaushatu yaceda,dakarunsa lallai babu watahanya sai mungifta tagaban dutsennan mai aman wuta sai yadaga murya yace lallai kowa yashirya domin xan aikata wani tsafi lallai xandakatarda wutar na tsawon dakika Sittin lallai duk wanda baiyi kokari yawuce adan wannan lokacinba to yahallaka nantake yafara karanto wasu sarkakkun kalmomi daga kalmomin tsafi damatsanancin Sauri yake Karantowa yarintse idanunsa yaigumi Sharkaf tundaga sama harkasa can akwarara tsawa mairudarwa saiSarki Kaushatu yabude idanunsa take wutantadauke aibaicema kowakomaiba sai yasaki linxamin dokinsa kamar walkiya yagilma hakasuma tawagarsa suka rika gilmawa suna wucewa amma tsananin yawansu saida lokacinnan yacika basugama wucewaba take dutsen yacigaba da aman wutansa yababbake wadanda suka rage Kowaige Sarki Kaushatu da dakarunsa basuyiba sukabi wata siririyar hanya maitsayi take wasu Aljannu masu sufar batoyi sukarika shawagi asamansu suna yunkurin daukansu sarki kaushatu yadagamurya yace yaku jama,ata lallai kadawanda yadaga kai yakalli aljannunnan koyai kokarin yakarsu xai mutuhaka sukaci gabada tsula gudu a yar karamar hanyarnan batoyinnan suna musu baraxana, Amma,al,amarin Boka Barnuhu da tawagarsa masu kokarin samama duniya,sauki sunutsa acikin tafiya domin su isaWadil Maut domin sumallaki Miyagun takubba tafiya suke babuSassauci kamar xasu tashi Sama suna keta kwaxaxxabo gamida haure duwatsu suna tsallake koramau da tsaunuka harsu isawata doguwar sahara mai tsananin xafida kuna saidasukai tafiya tatsawon sa,auku cur sannan sukawuce Saharan sai su hangi wani bahagondaji maitarin duhuwa dadogayen itatuwa gamida manyamanyan Duwatsu sunadab dashiga daji Sai Boka Barnuhu yakwarara ihu gamida tsawa yace yaku taron maxaje lallai kada wanda yakuskura yashiga wannan dajin cik dakaru sukaja linxamin dawakansu dawakai sukai turjiya gamida Haninya bayan ansami Natsuwa sai Boka Barnuhu yace yaku maxajen fama lallai kowa yashirya yagyara damaransa domin tunkaran mutuwa gamida shirya shirin Gumu Gimbiya Eela tace yakai babban boka shin wace masiface acikin wannan daji Boka Barnuhu yace akwai wasu arnan daji masu tsananin karfigamida taurinkai da jaraban tsafi sam basabarin wata bakuwar halitta tawuce tawannan daji lallai tarihi yanuna samada shekaru dari biyubaya babu wata Halitta mutum ko,aljan ko gungun dabbobi dasuka keta wannan daji batareda arnan dajinnan sun hallakasuba kod boka Barnuhu yagama wannan bayaniSai Sadauki Amirul Jaishi yakwarara ihu yace lallai yau tarihi xaikaryerayuka xasu salwanta kuma saimunma kasa ado dajini yadaga murya yace tabbas ko,amutu ko,airai saimunketa dajinnan mun wuce ai yanarufe bakinsa Sai aka kwarma wani ihu mai furgitarwa gamida raxanarwa kwatsam sai cincirundon arnan dajinnan surika futowa daga cikin dajinnan yawansu yawuce misali,girmansu yakaigirman katuwar Bishiya sunarike dawasu miyagun makamai marasa kangado bakakenekirin munana masu kamada aladu sukai sahusahu saimuxurai sukeyi gamida lashe bakunansu tabbas insun sami naman mutum bashakkaci xasuyi Sarkinsu Maisuna Karkuxu yadakama Su Boka Barnuhu tsawa yanamaicewa ku mazzaje lallaikusani bama yaki Saida dalili dan haka inamai baku Shawara daku juya kukoma baya kunemi wata hanyar mutukar kunason kucigaba darayuwa aduniya turkashi lallai maza basa daukan Raini aituni Yarima Fawan yadakamai tsawa yace kaimutumin daji karyanka tasha karya lallai babu abinda xaisa mukomadabaya saidai mugo gamida Gwabxawa karfida karfi dantse da dantse wanda xai mutu ya mutu wandaxairayu yarayu wohoho ai sai Sarkin,arnan dajinnan yahassala yakwarara ihu yaima Jama,arsa tsawa gamida ambato wasu kalamai marasa Fassara aisai Jama,arsa sukai Ihu sukaikan Su Boka Barnuhu Suma sukai kainsu ahassale kowani bangare na Ihu gamida kururuwa sukai taho mugama akai karambatan karfe jini yakwaranyeda tsoka afara neman ranjuna ashiga Kairuwa ranadankari nanfa ihun maxaje yawaita arnan dajinnan sukarikama maxaje kisangilla wani abintashin hankali sukuma kaifida tsini baya tasiri ajikinsu kaiya aikoda adaulokaci anawannan bakin gumurxu Sai arnan dajinnan suka furgita Dakarun Boka Barnuhu ran maxaje yabaci Sadauk Amirul Jaishi yakwarara ihu maraxanarwa wanda saida tai sanadiyar yaki yatsaya cik NIMA NAYI RUFARSHAYI
By Sawwama A.
Page 4.
A zaune ya sami hajiyar cikin shiga ta alfarma kyakyawar macece wace tsufarta ya b'uya cikin jin dad'i da kyan jiki fuskanta na d'auke da manyan idanuwa da dogon hamcim da take yawan hurashi hakan yasa hancin ya zauna haka a bud'e saboda sabon da akayiwa hancin saboda masifa.
K'arasawa yayi ya zauna a k'asan kujerar da take ya d'ora kansa a bisa cinyanta ita kuma tajiye jaridar da tun da ya shigo ta daina karantawa ta d'ora hannunta a kanshi tare da fad'in ya "akayine babana me kawun naka ya fad'a maka ina fatan ba matsalar wancan shed'aniyar yarinyan can da uwarsu ta gama zugeta bane?" Turo baki yayi cike da shagwab'a irin na tabb'arrun yaran nan yace "kai hajiyata ni wanne toh zan ansa sai jero min tambayoyi kike?" Shafa kanshi tayi tace toh yi min bayani a nutse" d'ago kanshi yayi ya sake turo baki yana wani shagwabewa yace " toh ba tace wai ni nayi mata yaro ba kuma ni d'an k'auyene kum...." A harzuk'e ta katseshi da fad'in a haifeka a turai ka taso a turai sannan ta kalleka tace maka d'an k'auye kuma ina batun yaranta yake a nan tunda ka mallaki hankalinka gaka da iliminka da sana'arka banda ka dagewa koyarwan nan daka sa kanka ga kamfaninka da mahaifinka ya bar maka amma a dubeka ace maka yaro d'an k'auye saboda tab'ewa da rashin rabo?" Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi dan shi d'in me yawan murmushi ne yace kin san 'yan Jos d'in nan in kana Bauchi ko wani gari na Hausa fulani d'aukanka suke d'an k'auye bagidaje saboda mu bamu d'auki d'abi'ar yahudawa ta sanya tufafi me nuna tsaraici da rashin sanin hakkin gabb'an jikin d'an adam kuma maganan yaranta tabbas ni d'in yaro ne shi ya sa kawu nema min mata k'aramar yarinya daidai ni...." Cikin k'araji ta kuma fad'in " me kake shirin gaya min in na fahimceka so kake kace min wancan k'abilar taci nasara a kanmu a karo na biyu kenan ta samu ta auri d'an uwana a b'agas sannan yanzu ta nemi hanamu had'a zumunci shi kuma wancan sallamamen sai biye mata yake yi har da wai ya samo maka mata a wani wajen" fuskantanta ya kuma yi da kyau yace " bafa a wani wajen ya sama min mata ba 'yar wajen sa d'ayar fatima ya bani." Hmm ta sauke ajiyar zuciya ba tare da tace komi ba dan ita gani kawai take an raina musu wayo ganin tayi shiru yasa ya cigaba da fad'in " shi yasa nake so kije ki sameshi a bar maganan nan da zuwa wasu 'yan shekaru dan ni ganin k'ak'antar yarinyan nake a bari zuwa ta gama secondary nima kafin nan na d'ora karatuna sai a ga abinda Allah yayi" yayi shiru ya zuba mata idanu yana me addu'ar Allah yasa ta yarda da hakan hikimarsa tayi hakan shine watak'ila in aka bar maganan zuwa wasu shekarun la Allah su daidaita ko kuma kowa ya had'u da abokin rayuwarsa a gaba danshi sam son da yake yiwa yarinyan na 'yan uwantaka ne toh ya ma zai iya mata wani so bayan nan yarinyan da take 'yar mitstsiya baya tunanin ko nono ta ajiye a k'irjinta, sai dai ina adu'arsa bata ci ba dan bud'en bakin hajiyar tasa sai cewa tayi " lallai kuwa Hauwa taci riba akaina ai haka take so uwar tasu dabarar ta kenan ai kaga itama wancan d'in in ta k'ara girma sai a hure mata kunne watak'ila ma ta nemi had'ata da wani birom d'in ko wani k'abilan nan cikin jos d'in ba dai aurene bata so y'ay'anta suyi a zuriyarmu ba ai kaman anyi an gama dan bazan yarda a wani d'au lokaci ba za ayi abinnan duk da ba wani son wancan yarinyan mai kama da zuriyar masu k'ananan ido nake ba dan yarinyan akwai falli in tace zata zo ta min halin uwarsu ni casa shegiya zanyi."
Rintse idanu yayi ya mik'e ya fice a palon ba tare da yace mata komi shi bai san ranan da hajiyarsa zata daina masifar ba gaira ba dalili ba ko me mamansu fatee tayi mata oho to ita fatin me ta tab'a mata dan dai kawai itace shugaban masifafun Bauchi tsaki yaja yana since kayan shi dan shiga ya watsa ruwa.
💖💖💖💖💖💖💖💖
Zaune suke a gaban mahaifansu inda baba yake magana da adeeja ya fara " ki gayawa shi manemin naki kwanaki 14 na bashi ya turo magabatanshi in ba haka ba kar in k'ara ganin ya kiraki a waya dan ni ban son harkar yaudara nayi bincike a kansa duk abinda kika fad'awa mamar taku a kanshi gaske ne saboda haka yanzu shi mike jira a tsai da magana nayi waya da hajiya zata zo ke kuma" ya juya kan fatima " na san ke kam d'iyace me biyayya na san komi na yanke a kanki ba za ki ban kunya ba shi yasa na yanke shawara akanki ba tare da ko mamanki nayi shawara ba saboda na san na isa dake" gabanta ne yake lugude yayin da ita adeejan duk ta muzanta dan ta san gugar zana yake mata duk da bata san me yake shiri faruwa da y'ar uwarta ba.
A cikin tsakiyar kanta taji yana cewa " na ba da auranki ga d'an uwanki sagiru" a firgice ta d'ago da kai sai kuma ta mayar da kanta k'asa tuno irin yabon da mahaifinsu ya mata kafin ya furta musu zance adeeja kam jin zancen tayi banbarakwai sai abin ma yaso bata dariya har sai da ta murmusa wai dole ne sai ya auri 'yar gidansu" baba ne ya cigaba da yiwa fatima nasiha ita kam sai hawaye take wanda ta rasa dalilin zubar hawayen dan ita baza tace tana k'in yayansun ba amma ita sam bata mishi soyayyan aure kukanta ba zai rasa nasaba da ya makomar karatunta yake ba wai shin ita dukka dukka shekarunta nawa da za a kinkimo mata magana aure anya baba na lissafin shekarunsu kuwa? Haka tayi ta sak'e saj'e har baban ya gama maganarsa ya sa musu albarka ya fice.
Mama ce ta matso kusa da ita tare da dafa ta d'ago kanta tayi wasu hawayen na zubo mata hannu maman ta sa tana goge mata hawayen tare da furta " Saahyu ra pfenda daramo( kiyi shiru kiyi abinda babanki yace) kinga in kika k'i y'an uwanku ni zasu zarga suce na hanaku aure a zuriyarsu a gabanki ranan hajiya ta kirani a waya tace ko nak'i ko na so ku yaransu ne kuma dole suyi iko daku dan basa yiwa yaransu auran dolene da ba abinda zai hana baba karami ya auri adeeja sai kace nice na hana adeeja ta aureshi kece yanzu zaki wankeni ki daure ki auri zab'in su zaki ji dad'i wata rana kinji" fad'awa jikinta tayi tana kuka tana fad'in ni ba wai bana so bane is just too early kaman kuna manta shekaruna i am just 15 years for goodness sake mah ko ina fulani i am not living like one is high time a daina wannan auran wurin(shekaruna 15 fa dan Allah ko da nake fulani ai bana rayuwa kamar bafulatana lokaci yayi da za a daina auran wuri)" gyad'a kai maman tayi tace " dagani har ke bamu da choice a gabanki yace baiyi shawara dani ba ya zartar da hukunci sai mu zuba musu ido Allah yayj zab'i ke dai ki daure ki bisu zaki ji dad'i ni na tabbatar miki da haka duk wanda yaji maganan iyayenshi ba ya tab'ewa zaki ci *ribar biyayya"* kad'a kai tayi tace" na miki alk'awarin ni kuma zan muku biyayya ko dan in wankeki a wajensu" murmushi mama tayi tace na gode 'yata Dagwi an nonwo wen homa neimo niraho (Allah ya miki albarka ya sa kema yaranki su biki) ameeen.
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
Page 5.
Hajiya tazo tare da baffannin su da kuma yayyun sageer da suke gari maneman auran adeeja sun zo an tsai da aure wata biyu dan baba ya rantse ba zata kuma yi mishi shekara a gida ba tunda ita bata jin magana taje can ta k'arata in mijin yaso ya mai da ita makaranta. Sageer da fatima kuma an tsai da magana da zarar ta gama jss3 bayan sallan azumi kenan hakan ya kawo cecekuce a cikin anguwa da dangin mama inda ake ganin an shiga hakkkin yaran har wani wan maman ke barazanan maka su a kotu sai da mama da ngo suka yi jan ido tukun wanda hakan bai tsirar da maman daga shan zagin hajiya ba tattas ta wanketa wankin babban bargo.
Bayan tafiyarsu hajiyar adeeja ta shigo d'akin inda ta tarar da teema na ninke kayan da ta wanke musu ( dan tunda taji su hajiyar zasu zo ta gudu daga gidan kar ta sauke mata kwandan bala'in tak'i d'anta) dariya ta kwashe dashi tace "su amarya manya tare da angon aka zo ne banga kina farin ciki ba 'ya mai biyayya ki zauna a kashe miki rayuwa wai ke zaki faranta ran iyayyenki toh bari in gaya miki ki shirya kamuwa da yoyon fitsari tunda kika zab'i aure a wannan shekarun kina samun cuta ya sakoki dan halin 'yan Bauchi kenan in bai sakeki ba ya k'aro aure another halinsu kenan ke kuma kin zama rajab ya tsufar da ke saboda nuk'urk'usa a daidai lokacin da nake shan love da hameed d'ina."
Bata kulata ba sai da tagama adana kayanta har da na adeejan tace " adda adeeja ni yanzu kin daina ban mamaki sai tsoro kin koma kamar ba musulma ba kin kasa yiwa iyayenki biyayya ni da nake k'ok'arin yi musu kina neman ki hure min kunne ta hanyan tsoratar dani wai kam kina tunawa da cewa mama kike sawa a matsala duk wani hali da kike yi? Ba abinda masifafiyar matar nan ke cewa da ya wuce kin zuqa kafirci a nonon uwarmu wanda ita mahaifiyar tamu ba a haifeta a kafirci ba sai dan kawai tana ansa suna yaren birom shikenan ake dangantata da kafirci kema kuma kina taimaka musu wajen b'llo da wasu halaye baki tsaya a iyakan k'in musu biyayya da tsoratani ba har mugun baki kike bina da shi a matsayinki na 'yar uwata wallahi ki kama girmanki tun kafin ya fad'i dan in ya fad'i ba abinda zai hanani hawa in tattakashi har da tsalle."
Shak'ota tayi tana nufin jibgarta mamansu ta shigo ta fizgeta a hannunta tace " kar ki yarda ki tab'a min yarinya ke in ba kya tausayina ita tana sona tana tausayina ace kece babba sannan kuma kece ba ki da hankali Allah ya wadaran halinki hadija" ta ja hannun fatima suka barwa adeeja d'akin.
💖💖💖💖💖💖💖💖
Asalinsu mutanen Bauchi ne malam salisu shine mahaifinsu yayinda inna sala itace mahaifiyarsu su biyu tak ne a wajen mahaifansu Hadiza itace babba ratan shekaru biyar ne tsakaninta da k'aninta mustapha suna k'anana iyayensu suka rasu sakamokan gini da ya fad'o musu sanadiyar ruwan sama da aka tsuga a lokacin yaran sunje gidan k'anin babansu baffa umaru.
Dole rik'onsu ya koma wajen baffan nasu da fari matar baffan ta so gwada musu mugun rik'o kasancewar hadiza yarinya ce me shegen tsiwa da masifa yasa ta shafawa kanta lafiya hadiza na gama primary aka hankad'ata GGC kafin madaki inda ta bar k'aninta wajen matar baffa tana azabtar dashi shima yana wayo ya k'arbarwa kanshi 'yanci.
Ranan da hadiza ta gama aji uku ana speech and price ta lashe mafi yawan kyautuka cikin manyan bak'in da suka zo alhaji musa ya nuna yana sonta bada jimawa ba aka sha biki ta tare a gidanta inda take rik'e mishi da yaransa maza biyu da matarsa ta mutu ta bari.
Haihuwarta biyu duk maza salis da mustapha alhaji musa ya sami aiki a america suka tattara suka koma can ba yanda bata yi ta tafi da k'aninta ba baffansu yak'i yace baza a d'aurawa bawan Allah nauyin da ba nashi ba can ta haifi salamatu da sagir mai sunan baban mijinta.
Shi kuma mustapha bayan gama secondary d'inshi ya sami gurbin karatu a university of jos inda yake karantan mechanical engineering yana shekara ta uku aka kama wani da satan ansa aka mishi cune aka koreshi. Bai gayawa kowa ba ya kama kanikanci a gada biyu nan ya had'u da hauwa yarinya birom cikakkiyar musulma ce gaba da baya sai dai zuriyarsu na cakud'e da marasa sallah baffa ya shige mishi gaba aka yi aure yayarsa cr ta had'o mishi lefe daga can ta aiko baffa shi ya hana a gayawa hadiza k'abilar da mustapha ya jajub'o kasancewarta mai kishin yare da addini.
Dawowarsu nigeria kuwa ba k'aramin artabu akayi ba dan fushi tayi da k'anin nata sosai wai k'aninta ne da aure wata k'abila har da rabon y'ay'a biyu lokacin shekarun fatima bakwai lokacin ne tazo da dukka ya'yanta gidan mustapha zuwa sagir na farko kenan yana d'an yaronshi ba k'ara zuwa ba dan shekarar ya shiga jami'a b'angaren k'iyayyar da hadiza ke yiwa hawwa kuwa sai abinda ya yi gaba.
Wannan kenan.
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
Page 6.
*Alhamdulillahi Ina mai mutukar nuna farin cikina hakika baka sanin masoyanka sai abu ya sameka na gode muku masoyana Ana mugun tare irin sosai din nan*
_Na manta a dalilin mutuwar alh musa ne yasa haj hadiza_ baro us
***** ******* *****
An tsai da ranan auran adeeja watanni biyu kacal Dan baba ya dage bazata karasa makaranta ba tunda ita bata ji.
Fatima da sagir kuma an yanke bayan sallan azumi dai dai da ta gama jss3 kenan watanni shida nan gaba kenan.
Adeeja da hameed sunfi kowa farin ciki cikar burinsu duk da adeejan na tausayawa yar uwarta halin da ake shirin jefata na aure da wuri sannan ga masifaffiyar uwar miji ga neman iliminta da ake shirin datseshi, dan ita tana da tabbacin hameed bazai datse mata karatu ba Dan sun gama shawarta suna aure zata koma tunda term daya ta rasa.
Sagir bai samu zuwa ya ga fatima ba kaman yanda aka tsara ba saboda yanayin koyarwarsa kasancewan ba a cikin gari yake aiki ba a wani private boarding school mallakin abokin abbansa yake koyarwan.
Hajiya bata son wannan nanatacen koyarwan amma ya dage shi abinda yake so kenan yayunshi sun shawarce shi yayi lecturing tunda yana sha'awar koyarwan yace ba yamzu ba sai nan gaba yafi son ganin ya fara from the very ground suka ki yarda dole ya fara daga secondary school.
Shi rashin samun zuwa jos ya mishi dadi Dan har ga Allah yana kunyan ya daga ido ya kalli yarinyan a maysayinshi wai na Wanda zai aureta haba! AI da kunya shi kanshi kunyan kanshi yake wai wannan tatsitsiyar yarinyan nan ne future wife dinshi inaaaaa ba zai taba iya nunawa wanda suka sanshi fatima a matsayin wacce zai aura ko matarsa ba.
Hmmm in dalibansa suka ji KO suka gan ta a matsayin matarsa ba karamin dariya zasu sha ba a irin yanda yake daure musu (awwn he wince) mussamman shegun matan nan masu shegen naci yara kanana sai son soyayya ya datsen halshensa da hakoransa kiransu yara da yayi dan ya San sun fi so called fiancee dinshi shekaru da komi da komi na fannin sura.
Bangaren fatima kam tafi baba karami fargaba da kunyan haduwa da shi mussaman in ta tuna sokoncin da take tayi a gabanshi da yanda take koda kyanshi da manyan idanunshi wani sa'in har rufe fuska take da tafukan hannunta KO in tana kwance ta tuno sai ta ja bargo ta rufu har kanta.
A haka rayuwa ya tafi har wata biyun da aka diba na bikin adeeja ya cika inda aka sha biki aka Kai amarya hajiya tayi rawar ganin wajen had a Mata kayan daki ingantatu sai fatan ta zauna lafiya da kishiyarta da mijinta a rikkos.
Duk kumbiye kumbiyen fatima da baba karami Allah ya kawo mu hutn second term dole baba karami ya dawo gida yayi shirin zuwa zance kuma dole fatima tayi shirin tarban ba konta.
Yana zaune a dining yana cin abincin hajiyarsa yayin da hajiyar ke zaune a babban Palo tare da babban dan mijinta da yazo daga America tunda shi aa can yayi auranshi duk da matarsa yar Nigeria CE amma haihuwar can girman can.
Tasowa yayi daga dining din ya dawo Palo ya zauna tare dasu.
Da kulawa hajiyar ta dubeshi tace "babana yaushe ne zuwa jos din? "
Dan yamutsa fuska yayi yace "wai hajia dole sai naje ne ba bikin saura 4 months ba? "
Rike baki tayi tace dole kai AI dole kaje babana saboda mu nunawa wancan da gaskenmu muke ba Zan Bari ta rabani dan uwana Ba, kuma itama yarinyan ba sake mata zaka yi ta raina ka ba dan naga kan na rawa kaman na uwarta.
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
Page 7.
Dakin ya dau shiru na dan wasu sakonni kafin daga bisani alh ashiru baban yayansu baba karami ya katse shirun da fadin "wai ni kam hajiya ba anyi hadin nan dan a kara dankon zumunci bane?" Ba tare da ya bata daman amsawa ba ya cigaba da fadin " toh menene xaki ce kar ya sakewa yarinyan da zai aura fuska? Ba sai an sake fuskan bane za a samu fahimtan juna? Dan Allah.hajiya.ki daina barin abinda ke tsakaninku manya yana shafan mu yaranku.
Duk da itama matan uncle din ba wai ta miki wani abu bane,laifinta daya a wajenki dan ta kasance wata yare which is not her fault beside hajiyarmu hausa,fulani,jarawa birom,angas,yoruba igbo duk daya muke a wajen Allah kuma shi ya hallicemu kuma yana sonmu matsawar muka bi dokokinsa, hausa fulani bai fi birom ba ba wanda ya fi wani a wajen Allah sai wanda ya fi tsoronshi.
Ganin yanda take muzurai sarai ya san ya kunnota fushin nata ya motsa da sauri ya juya ga d'an uwanshi yace "kanina bari in baka wani hadith _akwai wani mutum ya taba zuwawa ma'aiki yace yah rasulillah ka min wasiya sai annabi yace masa kada kayi fushi_ sai da annabi ya nanata sau uku. Me yasa annabi ya mana wasiya da cewa kada muyi fishi saboda mafi yawan hasara dukka tana zuww da fushine. Kaga yana da kyau mu dinga controlling fishinmu.
Fuuuuuuu ta tashi ta shige d'aki dan ya riga ya daureta da sauri baba karami ya kankame dan uwanshi yace wallahi babban yaya kafi kowa iya zama da hajiya pls ku tattaro ku dawo nan.
Murmushinsu na manya yayi yace ba dai mu dawo ba kasan auntynka ba yarda zata yi da zaman nigeria ba amma zanyi kokari mu zo azumi har zuwa bikinka.
Murmushi kawai yayi.
Washegari da yamma baba karami ya shirya zuwa jos zuciyarsa cike da fargaban ya zai fusakanci fatima.
Tana zaune mama na tubke mata gashinta mara cika sai dan tsaho da yauki sosai tsawonshi a bisa dokin wuyanta ya tsaya injita tace komi nata kadan😜 wayar mama tayi ruri da sauri ta daga cike da ladabi ta gama ansa wayan kallon fatiman tayi tace "fatima maza tashi ki kimtsa baba karami na hanya ki share mishi dakin zauren
Dam gabanta ya fadi jiki a sanyaye ta mike ta canza kaya tunda dama tayi wanka ita abin wani iri yake mata toh wai kwalliya zata yi kai ah ah ai sai yaga zakewarta powder ta shafa da man baki.
Dakin zauren ta share ta saka turaren tsinke kafin ta koma daki zaman jiranshi tare da fargaba dama haka ake ji in za a zo wajenka zance kai ah ah duba da yanda adeeja ke rawar jiki in hameed zai zo tayi tq kalkale jikinta kenan jikinta har rawa yake sabanin ita da take jin mutuwar jiki da faduwar gaba.
Gabanta ne yayi mummunan faduwa jin muryarsa a tsakar gida suna gaisawa da mama, maman ce ta umarceshi da shiga dakin zauren shi kanshi jin sh wani iri yake shine da zuwa zance wajen fatima.
A hankali ta shiga dakin bakinta dauke da sallama ajiye tray din hannunta dake shake da abinci da na sha tayi kafin ta zauna tare da lankwashe kafa cikin rawar murya ta gaisheshi, bai amsa ba sai zuba mata ido yayi ganin duk yanda ta duburburce sai gyara zama take tana jan gyalenta da ta rufa a kanta wai yau fatima ce da kunyarsa ko da yake shima cike yake da kunyanta amma duk zai musu maganin abin
Bintoto ya furta cike da zolaya itama a hanzarce ta dago kanta jin sunan da yayi kiranta da shi ido ta zuba mishi ganin shu'umin murmushin da yake yi lokaci daya suka fashe da dariya dan tsagaitawa yayi da dariyarsa yace ko ba sunanki bane bintoto? Gyada kai tayi tana kokarin hadiye dariyarta tace " ah ah fatima zahra nake meye kuma wani bintoto?
Zo ki gani ya yafitota da hannu yana kokarin ciro wayarsa da dayan hannun youtube ya shiga ya searching abinda yake nema dariya tayi sosai dan ta manta ma matsayin da yq zo mata cikin dariya tacr Allah sai na nemi kaset din wakan nan na kalla.
Murmushi yayi yana kallonta yaji dadi fa wancan tension din ya fita a tsakaninsu fatima ya kira sunamta a nitse dago kanta daga kallon wayan tayi tana mishimurmishi
Ajiyan zuciya ya sauke yana kimsa maganan da zai furta mata Allah yasa kar ta mishi munmunan fahimta ta fassara shi
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA 💖
By Sawwama A.
Page 8.
"Fatima" ya kira sunanta akaro na biyu wanda hakan shi ya ankarar da ita ta nutsu.
Fatima kinga hukuncin Allah ko? Iyayyenmu sun yanke hukuncin aurar damu ga junan mu ba tare da la'akari da kankantan ki ba. Ina so ki cire duk wani fargaba a ranki na aurena ki dauka kaman in anyi auranmu zaki bar nan gidan na wasu yan shekaru ne ki tafi karatu bauchi, a lokacin da kika mallaki hankalinki sai muga abinsa hali zai yi a wannan gaban ne za mu yankewa kanmu hukunci kin fahimceni?
Gyada mishi kai tayi ba tare da ta fahimceshi din ba. Good yanzu ina so kisaki jikinki da ni mu cigaba da kasancewa kaman da kar mu bari abin nan ya taba dangantakar mu nan ma ansa mishi kawai tayi a hankali ya cigaba da janta da surutu kafin wani lokaci har ta saki jiki ta ffara biye mishi ta fara shiriritar na ta.
Sosai iyayyenta suka ji dadin ganin yanda suka saki jiki da juna suna harkokinsu a nasu zaton sun rungumi juna suna soyayyarsu ne sabanin su da suka manta ma wai za a musu aure tare.
Kwanan baba karami biyu a jos a kwanaki biyun nan shaquwarsu da juna ya kara habaka inda ya dinga daukanta suna zuwa outing ya bi ya mata siyaya ya so siya mata waya amma sai ya duba kankantata wa ma zata kira kawai sai ya sai mata mp me kyau da tsada yace asha jin kida da karatu dai, dariya kawai tayi haka ya musu sallama ya koma bauchi.
💖💖💖💖💖💖
Akwana a tashi asarar me rai har su fatima sun gama exams an tsunduma cikin shirin biki ita kam kallon abin take kaman shirin film ko littafin hausa sai dai ina a zahiri ne kuma a kanta ne, mutanen anguwarsu ta alheri sun cigaba da cece kuce akan batun auren da suke kira child abuse sai dai wasu daga cikinsu basu yi mamaki ba kasancewar sun san fulani da auren wuri sai dai sunyi zaton ai tuni an daina wannan yayin a dauki yarinya da bata gama rika ba a kaiwa wani kato yayi ta sassaka sun manta su nasu ya'yan da basu wuce 15 years ba sun iya su bude ma wani kato kafa saboda naira dari da zasu sai plate of rice Allah shi kyauta amin.
Abin mamaki baya karewa duba da yanda adeeja take wani shige da fice a auren sune kan gaba sai wani iyayi take tayi kyau sosai tayi hasken amarci dama tafi fatima kyau nesa ba kusa ba dan ita manya idanu gareta kaman su baba karami sabanin fatima da nata ba manya bane amma a waje suke basu shga ciki ba dogon hancinsu daya da karamin bakinsu kuma ita tana da diri tunda ta zama cikakkiya budurwa sabanin fatima da nonon ma yanzu suke fitowa kuma da alama ba mai manyan nono bace dan adeeja na da shekarunta nononta ya fi na fatin.
Fatima bin kowa take da ido yanda ake ta hidima kaman bikin wata babbar budurwa bata san aure sunanshi aure ba adeeja ce ta shiga kan nan na rawa tace ke kuma amarya baki tashi kin shirya ba wai ina kayan fitan biki ne da hannu ta nuna mata kayan da baba ya bayar a dinka mata da sauri ta karasa tana dagawa juyowa tayi tana kallonta kafin daga bisani tace wai kina nufin kayan da baba karami ya kawo kenan tace ah ah baba ya kawo min su.
Zama tayi a gefen gadon inda fatima ke zaune tace wai duk kudin su yah sagir din nan bai baki kudin kayan fitar biki ba bai kuma kawo ba? Wannan wani irin bikine ko event daya ba fa ayi ba ban nombanshi tagumi fatiman ta zuba tace ni ban da ita ki kyaleshi mana wadannan sun isa wallahi.
Harara ta wurga mata tace anki a barshi shegiya ke kike mishi da sauki ashe ta fita ta karbo number dan rashin kunya ta kirashi yana kwance yana baccinshi wayarsa tayi ringing kaman ba zai dauka ba kasancewar bai san numbern ba amma nacin kiran yasa ya dauka cikin karadi tace kai yah sagir kaman ba zaka dauka ba adeeja ce.
Sai da gabansa ya fadi ya dake yace ah ah mamana ya kike ya mijinki? Lafiyanmu lau gani nayi har gobe daurin aure bangga kayan fitan bikin amaryar taka ba ga shi ban ga kun shirya mana wani biki ba. Dan duburburcewa yayj dan shi sam ya manta wai gobe zai zama ango kuma shi bai san ana wani kayan biki ba event kuwa shi wa ya aikeshi hada wani taro a ga aamrya kamar yar yaye.
Hello kana jina ta katse shi, yeah yeah ina jinki ai naga ana kawo akwatina yau suna bisa hanya ma kuma naga kaman akwai dinkakun kaya a ciki kin san ni ban san ya ake yi ba kuma bata gaya min ba event kuma ni ba wasu abokanai gareni ba ai da kun shirya na family.
Haka ne kam Allah ya sa akwai dinkakkun ayi hidima lafiya ta katse layin ajiyar zuciya ya sauke yana me jinjina karfin halin adeeja ko ni na jinjina rashin kunyanta kice ba kya son mutum ki kuma zo kina kara nuna mishi auranshi da kanwarki be dadaki da kasa ba Allah ya kyauta.
Mutane sun gigita da dimbin kayan da akayiwa fatima kaman na wata big girl under wears da lingering bra ubansu ko a wani nonon za a sa oho😁
An daura aura an kai amarya gidanta dake cikin gidan hajiya a bauchi inda a daren hajiya ta hada mothers night aka ci aka sha aka watse aka bar amarya da angonta sai fatan Allah ya zaunar dasu lafiya su ci ribar yiwa iyayensu biyayya.
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
Page 9.
A hankali yake kutsa kai cikin sashin yana tafe yana tina kalamen mama a gareshi. _baba karami ga amanar fatima,yarinya ce karama da bata san komo ba dan Allah ka sa tausayi a zuciyarka kafin bukata_murmushi yayi a hankali me hakan ke nufi mama tana gani zai iya sauke buqatarsa akan fatima ne?
A hankali ya tura kofar dakin da yafi tunanin tana ciki. A takure ya sameta tana bacci tana zaune a kasa ta daura kanta a kan gadon karasawa yayi ya dan tapping dinta a firgice ta farka kasancewan daman a tsorace take, tana ganin shine ta fashe da kuka tare da fadawa jikinshi.
Hannu yasa ya rungumota da kyau yana shafar bayanta yana fadin "shshshhhhh issokey yi hakuri nayi zaton sun barki a gefen hajiya ne da na shigo tuntuni ai sorry ko cikin sheshekan kuka tace yah sagir tsoro nayi ta ji ni kadai fa gidan ta min girma. Daga girarsa yayi daya wai gidan ya mata girma dakuna biyu ne fa wanda ko wanne ke da bathroom sai palo da kitchen ko dining area babu. Sorry my sister bazan kara barinki ke kadai ba kinji? Ta gyda mishi kai kinyi sallah kuwa tace ah ah na kasa tashi inje inyi ina ta jin tsoro
Yace ok ina zuwa drawer ya bude inda aka jera mata kayanta kayan bacci ya ciro riga da dogon wando sai hula da hijab ya miko mata yace tashi ki shiga kiyo wanka tare da alawla ina jiranki karban kayan tayi ta marairaice fuska tace yah sagir dan Allah kar ka fita ka barni murmushi yayi yace bazan fita ba turo dan bakinta tayi tace ka ma fita na san me zanyi in rama baba karami nima zan koma ce maka dariya yayi yace bazan fita ba yi maza kije kiyi.
Yana zaune a dakin har tayi wanka ta fito sanye da kayan da hijab bayan gidan ya shiga ya watsa ruwa tare da yin alawla tunanin yanda zai daura towel.ya fita yake yi idonshi ya sauka kan rigan wanka hamdala yayi ya saka har lokacim tana sallah kila shafa'i da wutiri take fita yayi a dakin ya shiga nashi da sauri ya fitar da kayaking barcinshi ya zira wando yana kokarin sa riga ta fado dakin kaman wanda aka koro da sauri ya karasa zira rigar yana fadin yi hakuri nima kinga shiryawa nazo yi zo muje ya riko hannunta suka fita palo inda ya ajiye ledar da yayunshi suka bashi dan shi sam bashi da abokai yayunshi ne abokansa da hajiyarsa.
Kitchen suka je suka dauko plate da cups suka koma dakin sallah yaja su yana tune da yanda yaah ashir ya dinga jadada mishi sallar nan duk da a kasan zuciyarshi ya sb bazai kusanceta ba amma ya kudurta yin sallan, bayan sun idar ne suka sha fresh milk da kajin da ya shigo da shi a daddafe saboda baccon dake fisgarsu.
Yau kwananta uku a gidan daki daya suke kwana saboda fitinanan tsoronta dan ko a jos bayan auren adeeja charity ke zuwa tayata kwana. Yau tun asuba ake tsuga ruwa bacci suka koma bayan sun yi sallah
Bata tashi farkawa ba sai goma har lokacin ana yayyafi ga wani sanyi da ya sauko tura baki tayi ganin ita kadaice a dakin wanka tayi ta dauko wasu riga da wando na sanyi ta saka ta dauko hulan sanyi ta saka shi har lokacin bata daina jin sanyin ba a fili tace kai sai kace muna jos palon ta fito tana goga tafukan hannunta yana zaune sanye cikin dogom wandon track suit da armless riga hannunshi rike da cup yana sham tea.
Zama tayi a one sitter tana ciggaba da goga hannunta tare da hura iskan bakinta me dumi "yah sageer ina kwana? An tashi lafia ,ya sanyi? Gira daya ya daga yace "wai irin wannan dogon gaisuwa toh duk lafiya" dariya tayi tace da kyau, wai kai kam baka jin sanyi ne ji yar rigar da kasaka? Kallon jikinshi yayi ya kalleta yace kenda kika tila wannan uban kayan ma baki fini jin dumi ba. Gyada kai tayi tana cusa hannunta tsakanin cinyanta tace Allah sai kace watan sha biyu ko watan daya a jos.
Ganin yanda take takurewa ya sa ya mika mata hannu yace zoki ji dumi tashi tayi ta karasa ya sata a jikinshi yace b abinda ya kai body contact saurin kawar da sanyi ita dai gabanta sai lugude yake dan ko da suke kwana daki daya bai cika kai hannunshi jikinta ba sai da dalili.
Sunyi kusan five minute a haka wani tunanine ta ziyarci kwakwalwanshi yace jeki hada tea kizo zamuyi magana jikinta a sanyaye ta tashi ta hada tea din ta dawo.
Sai da ta gama ya fuskaceta yace fatee kin san na taba gaya miki zamu yi zama ne ba irin zama na aure sai dai zama na yaya da kanwa ta gyada kai yace good nan da kwanki goma sha makarntar da nake koyarwa zasu koma hutu kuma tare zamu tafi sai dai ke a mattsayin daliba zaki kuma kanwata dan haka.nace musu ko da wasa ban yarda sabo yasa kiceqa wata wai ni mijinki bane mu yan uwan junane har abada kin fahimta? Nan ma gyada kan tayi kaman kadangaruwa yage yawwa bintoto dariya tayi tace aha baba karami shima dariyan ya tayata yace zaki sani ba dai kin rainani ba hannayenta ta hada tace ah ah ba raina yayana ba.
Cikin kwanaki bakwai wata shakuwa ce ta shiga tsakanin baba karami da fatima kasancewarshi mutum mai saukin hali ba girman kai a tattarre da shi haka zasu yi ta wasan guje gujensu a dan palonsu ko su kunna waka ya riketa suyi ta rawa har rawan tuawa yake koya mata yana bata labarin lokacin da yake america da budurwarsa ta high school da wace yaje prom night da ita tayi tq dariya yayi mata alkawarin in har tayi kokari a makaranta wata rana zai je da ita.
Plate din abinci ne a gabanta ta tabe baki tana shirin kuka gefe daya baba karami ne ya hade rai kaman bai taba dariya ba zata iya rantsewa wannan shine karo na farko da ta gamshi a yanayin nan cikin kakkausar murya yace kin san Alllah sai kinci abincin nan dubeki ba ko auki kuma karatu zaki fara amma ba kya son cin abinci cikin shagwaba tace yah sagir kaifa ka cika min ciki da madarar shanu kuma ace sai na cinye abincin nan yana shirin daka mata tsawa dan yaga alama sai yayi da gaske salallamin hajiya ne ya katse shi tace tabdi lallai auta kace raino kawai aka bakaa kara karewa fatima kallo take yi sai yau ta kara ganin yarintarta yarinya ko nono bata da shi sanye take da gajeran wandon jeans da rigga mai dogon hannu ta kama gashinta in a pony tail stayle yarintarta ya fito kararaa takaici ne ya kumeta amma wallahi an cuci autanta "haba dole uwarta ta yarda a hada auran nan tunfa ta san rainon yarta za a mata kai baba karami rabu da ita kar ta ci abincin ba cikinta bane" shaggwab fuska yayi kaman bashi ke mazurai yanzun nan ba yave kai hajiyata ya zan barta bayan hakkin ci da ita yana kaina to ba gashi ka wadata tada abinci ba ta juyo ana zabga ma fatima hararra tace ke wato baki san kizo ki gaisheni ba ko? " turo baki fatima tayi tace inzo ki cika min kunne da masifarki la'ila la illallahu tunkaro fatiman tayi ita ko ta fece da gudu ta shiga daki tana dariya baba karami ma dariya abin ya bashi yana jinjina rigimarnfatima da kyar ya lallashi hajiyar ta koma gefenta shi kuma ya tunkari dakin fatiman.
SAWWAMA QAWWAMAA
BANGON DUNIYA PART 1C¥ Bakidaya dakarun aljannu da mutane sukai mubaya,aga Sarki Kaushatu dan,kan,ana yadubesu yabushedadariya yace lallai kunacikin yardata kumakuna cikintsarona take maxaje sukahada Sahu Sarki Kaushatu yace kowa yasaurara yanxunnan xamu sanya fararen aljanu kwararru afanni yankayi ateku su Tsunduma tekunnan domin Dauko Sarkar ajali take yasabi karanto wasu kalamai na surkulle take saiwasu aljannu masumutukar tsawo suka bayyana yawansu yafi karfin irga sukai gaisuwa Ga Sarki Kaushatu Yacekai gwanayen Ruwa lallai kuwatsu acikin tekun Bahar Xum kunemomin Sarkar ajali atare aljanunnan sukace angama Jikan Kurungu kawaiSaisuka afka cikin ruwanan take sukunna nutso cikin ruwa akadaina ganinsu take Ruwan tekun yarika toroko yana ammbaliya aljannuna sukadama ruwannan yai bakinkirin saida aljannunnan sukadauki tsawon sa,a uku sunaneman Sarkan ajali amma babu labari suka futo babbansu yadurkusa agaban Sarki Kaushatu yace kagafarcemu yashugabammu lallai munxagaye ilahirin wannan kogi amma babu alaman Sarkan Ajali acikinsa aisai Sarki Kaushatu yakwarara ihu yace karyane lallai yau komai dake cikin wannanteko sai yabayyana take yasabi karaonto tsatsuba yanacika yana batsewa yanawani damdam yafara canxa kala yaibaki yai kore idanunsa sukai jajur sai yatakarkare yafasa ihu yanuna tekun dawata jar sanda dake hannunsa dankari Tsafi gaskiyar maishi take wani jan haske yafita ajikinsandarnan yafantsama acikin tekunnan take ruwan kogin yakama konewa yana tsotsewa sannu ahankali sai anemi ruwannan akarasa tekun takekashe kaikace anshekara darine rabon goginda ruwananfa jamar,aljannu da mutane sukasha mamaki gamida tsorata domin ganin manyamanyan halittun ruwa kananansu da manyansu sunbayyana tsiraransu akwaryan tekunnan take Sarki KAUSHATU yadakama halintunna tsawa yanacewa kai kananan kwari kukoma bisa tudu domin xangabatarda binkice take halittunan sukai waje Sarki Kaushatu yajefa wani Farin Dutse atsakiyar tekunnan kawai sai Wani hoton katon kifi yabaiyana acikin Haske saigashi yabaina lokacin da Sarkar ajali tafada tekunnan wannan kifinne yahadiye sarkan kuma yafuta aguje dawani irin sauri tafiya tamkar walkiya tsabar tafiyar Kifinnan yana gudun Sa,a biyar acikin dakika,biyar, sai hasken yabace Sarki Kaushatu yakwarara ihu yace yaku jama,ata Tsinannan kififi Maisuna Surkum shineyahadiye Sarkan ajali lallai tafiyarsa tainisan banmamaki domin shu,umin kifine akwai wasu Shaidanun,aljannu guda bakwai dasuke taredashi sune suke ixashi ahalin yanxu yatunkari Bahar Jabal lallai muna bukatan mukama Wannan kifi kafin ya,isa Bahar Jabal domin gurine mai mugun hadari Sarki Kaushatu yaitsawa ga jama,asa yace maxaje kufara kera jiragen ruwa domin mubi bayan Shu,umin kifi Surkum, takeruwan kogin yadawo halittunciki sukoma inada aljannu da mutane suka fara kda manyan bishiyoyi domin kera jiragen ruwa Acan Kasar Sham kuwa sarakunan kasashe Dubune suka taruababban dakin taro domin tattaunawa akan Bayyanar Sarkan ajali lokacinda Sarakuna suka xaxxauna Sai Sai Sarkin Kasar Sham maisuna Sarki Jahuru yamike bayan yagabatarda Gaisuwansa ga manyan Sarakuna da manyan bokaye da maxajem fama Sai yafara bayani yana cewa yaku Taron Sarakunan duniya masu kaunar xaman lafiya dakwanciyar hankali lallai kusani Tsinannu bokaye sunkunnoma Duniya bala,i tahanyar bainama Al umman aljannu da mutane cewa Duk wandayamallaki Sarkan ajali xai shahara kuma xaitunbatsa saiyagagar kowa aduniya akarkema saiyamallaki duniya atafin hannusa sai yajuya mutane da,ajannu sanransa, tokusani tundaga ranar datsinannun bokayennan sukaima duniya wannanshela Shaidanu da aljannu dodanni da mutane dakuma nau,in hatsabiban halittu dabazasu irguba suka baxama gamida watsuwa adoran kasa karkashin kasa cikin koramu rafuka dakuma tsuburai da manya manyan duwatsu sakoda Lungunan wannan Duniya suna neman wannan Sarka amma saida sukai shekaru dari hudu sunaneman wannan sarka ammababu wanda yataba koda kuskurenganinta harwasu sun hakura kwatsam sai wani tsinannan aljanni mainaci da tsanani binkice yasamota towannan al,amari shineyakara bijiro da wutar masifan datanemi takwantawa domin hatsabiban sarakunan aljannu da mutane bokaye da Sadaukai sun watsu adoron kasa danmallakar Sarkan ajali Gashi annobar Duniya yabayyana Shima yashiga sahunneman Sarkan wani Jarumi yamike yace ya sarki Jahuru shin wanene annobar duniya Sarki Kaushatu yace jinka bala,i saninka masifa Sarki KAUSHATU DN KAN,ANA TUNKU MAI KAI YARO MAKISA jikan Sarki Kurungu Dankari ai jin an ambaci wannan masifa sai Jama,ar taron bakidaya suka mike gamida bude baki cikin tsananin tsoro da fargaba Sarki Jahuru yace yakujama,a yanxu menenemufuta wace hanya xamubi domin kubutarda Duniya daga fadawa bala,ida masifa Shiru babu wani mai motsi can sai wani boka dattijo shekarunsa xasukai dari dahayani yanasanya dadoguwar riga yanadatarinkasumba fari sol yanarike wata bakar Sanda yamike yace nine Boka Barnuhu ibn Marhu nakasan Jumki yacigabada cewa lallai masifa tatunkaro duniya kuma dole mudakatarda ita yace lallai yaxama dole muma mufuta neman Sarkan ajalikamar yadda shaidanu suka baxamanemanta idan harmukai nasaran mallakarta to munceci duniya daga fadawa Masifa sarki jahuruyace to xamu futane bakidayammu koko yaya Boka Barnuhu yace aa Zamu hada tawagace nadakarunXumunci ta futantun jarumai sadaukai goma Shabiyu Wani sarki yamike yace kowa yana bukatan futa wannan aiki tayaya xa,asami Mutun shabiyu Boka Yace xa,afudda dakarun Xumuncine tahanyar gasasarkin yacewace iringasa Boka yace dukmai sha,awar kasancewa aciki tawagar
BANGON DUNIYA
Littafi na Daya 1
Na Ibn Abdullahi
Complet
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.com.ng
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.com.ng
Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
,,,,#BANGON;;;;#DUNIYA PART 1A,Bayan gushewan yakin Duniya bayan mutuwar sarki Kurungu kura maicefanen almuru birida gatari kashemegona kowa yabishi xaiyi asara inbayi takudiba toxaiyi taransa duniya taxauna lafiya andaina yake yake Bayan gushewar shekaru tururu sai abinjiya yadawo xubadda jinI yayawaita yake yake yawanzuakowani sassa na duniya hakan tafarune sakamakon kururuwan bokaye cewa akwai Sarkan Sarki Kurungu tafadi ayanki Nahiyar Shammace yayin fadansu nakarshe da samarin askandariya itawannansarka itace sirrin sarki kurungu Karfinsa tsafinsa hatsabibancinsa duka,sunta,allakane awannan shu,amar sarka Masana suntabbatarda cewa badan Axifaa tainasaran cire wannan sarka awuyan Sarki Kurunguba toda baxatai nasara akansaba komai tsanani tofa shine bokaye sukai Shelaaduniya cewa duk wanda yamallaki wannan sarka na Sarki Kurungu mutun ko,alja tofa xaixama gagarabada kuma sai yagallabi aljanu da mutanen duniya sannan sai yamulki duniya bakidaya dankari wannan furuci shine yahassala maxaje gamida tunxura manya jaruman duniya bokaye sarakuna aljannu da mutane suka kwallafa ransu akan wannan Sarka sukai rantsuwa sai sunmallaketa koda xa,amaimaita yakinduniya sannan xasubi Sarkan dun inda tadosa kodako Takai BAGON DUNIYA Dan daxon sadaukan aljannune suka sauka adajin nahiyar Shammace domin mallakan Sarkan sarki gurungu, sarkace memutukar hadari domin dayawa dagacikin mutaneda aljannu sunganta amma abin takaici daga sukaimatahannu xasudauka sai tabace kokuma mutum yakama da wuta take zaikone kurmus wani gawur tacce aljani mai suna Gusruf yasauka anahiyar Shammace inda yakama neman Sarkan shida tawagarsa inda suka dukufa wajen neman Sarkan saida suka shafe kwanaki dari tara da sittin suna binkican Sarkan kwatsam alja Gusruf yai arangamada ita akogon wani Dutse yamika hannu xaidauka Sai sarka tarikida taxama,kumurcin maciji takawo mai sara caraf aljani Gusruf yakaima macijin raruma yadamki kan maciji dankari aisai yaji kamar yadamki wuta wani masifaffen xafi yarashi bisa tilas yasaki maciji Baidandarabayakaima macijin raruma yarikida yaxama wani murgujejen xaki namma aljani yafadamai kai saida Sarkannan tarikida sama dakala dari daga nau,in abubuwan bantsoro amma aljani Gusruf yaki tsorata,yature sai yadamki sarkannan akarshe Yainaran rike Sarkan tatabbata ahannunsa Yajiwani sabon karfi yashigeshi yajicewa kamar xai iyayakan mutanen duniya aisai yatakarkare yakwarara ihu ihunda yakarade Duniya bakidaya Duwatsu sukamafarfashewa bishiyoyi sukarika kakkaryewa rafuka sukarika toroko sunatsiri asama dabbobi aljannu damutane suka shiga ciki tashin hankali lokacin da aljani Gusruf yabayyanaafili sai aljanu sukarika yimasa sujjada inda namun daji suka kewayeshi alfahari yashigeshi girmankai yakamashi yaji kamar shine ke mulkin duniya totundaga rananda,aljaniGusruf yamallaki wannan sarka yashiga tashin hankali domin miyagun aljannu da shaidanun mutane marasa adadadine suka rika kawomai hari domin surabashida Wannan Sarka watarana yana cikin tafiya sai yaji ankira sunansa yawaiga sai yai arbada Mahaifiyarsa tana xubar hawaye Gusruf yanufeta damurna yanacewa kiyi farinciki mahaifiyata naxama xakaran duniya dominnamallaki Sarkar ajali Sarkar Sarki Kurungu maiduniya mahafiyarsa tadakamai tsawa tace kaiwawa mahaukaci lallai katsaya a indakake kada kariso guna kagogamin masifaGusruf yace haba mahaifiyata keda xaki murna meyasa xaki nuna bacinranki tace kai wawane yakaidana inamai baka umurni amatsayina na mahaifiyarka lallai kajefar da sarkannan aljani yakwarara ihu yace ina baxai yuwuba tace tokuwa xaka mutu kasani yakai dana lallai ita wannan sarka babu wanda xai iya kwanaki talatin da ita batareda ya hallakaba tabbas hatsabibancin sarkan da kwankwaman dake jikinSarkan,yawuce sanin mutanen duniya Aljani Gusruf yace to,itakenan babu wanda zaiyi amfanida ita bayan mutuwar sarki Kurungu tace akwai mutukar xaka iya tsira daga miyagun harin da jama zasukawoma natsawon kwanaki talatin tokuwa Sarkan xata xama mallakinka har abada saidai baxaka iyaba danalallai akwai manyan sarakuna da hatsabiban bokaye da jarumai da sadaukai mata da maza dakuma miyagun halittun duniya daga jinsin mutane da aljannu daxasu tunkariduk wani mahalukin da Sarkannankehannunsa tadaga murya tace tabbas babu wani mahaluki daxai iya kubuta daga sarrin wannan miyagu halittu naduniya Aljani Gurdus yakalli sarkannan yakalli,mahaifiyarsa yace yake mahaifiyata Shin,ita wannan sarkan a,inatadace daxama aljana tace zata xaunane kawai awuyan wani karamin yaro maisuna KAIRUF shima kuma zata xaunane awuyansa domin shine xaikaita maxauninta jurhum, aljani Gusruf yace inane Jurhum tace wani kogon tarihine dake BANGON DONIYAaljani Gusruf yace shin yaron jarmine ko hatsabibine koko wani Shahararran matsafine aljana tacekasani yakai dana shi wannan yaroba jarumibane kuma ba matsafibane sannan baida wata hatsabibanciko baiwa aljani Gusruf yakwarara ihu yace haba mahaifiyata tayaya xaikubuta daga sharrin sarakunan aljannu da mutane sadaukai da Jarumai miyagun halittu duk bazasu kyaleshiba aljana taidariya tace tabbasyaro kairuf xaikasance cikin masifada bala,i gamida tashi hankali tabbas matsafa da sarakuna zasudanamasa tarko domin bokaye Suntabbatar dacewa duk sarkinda yainasaran kame yaro kairuf har yaron yaikwanaki Talatin amasarautansa to sarkan zataxama mallakin wannan Sarki Aljani Gusruf yace tokuwa Kairuf baxaiyi nasaran kai Sarkan BANGON duniyaba Aljana tace zaikaita Domin xaisami kariya daga wasu jaruman maxaje bakwai wanda akemusu lakabida DAKARUN ZUMUNCI tabdiiijam nayi kicin#
Subscribe to:
Posts (Atom)